✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban APC a Zamfara

Masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da shugaban mazaba na APC a Zamfara

Wasu wadanda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da shugaban mazaba na jam’iyyar APC a karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfara, Sani Dangwaggo.

Mazauna yankin sun tabbatarwa da Aminiya cewa maharan wadanda ke tafe a kan babura sun wuce kai tsaye zuwa gidan shugaban jam’iyyar tare da tafiya da shi wani wurin da ba a kai ga tantancewa ba.

“Bayan sun zo kauyen, sai suka wuce kai tsaye gidansa inda suka dauke shi ta karfin tsiya a kan daya daga cikin baburan nasu ba tare da sun ji wa kowa ko da kwarzane ba,” inji majiyar.

Majiyar ta kara da cewa shugaban da aka sace din kuma dan uwa ne na jini ga tsohon kwamishina a jihar, Bello Dankande wanda shima aka sacewa ‘ya’ya a kwanakin baya.

To sai dai yunkurinmu na jin ta bakin kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar SP Muhammad Shehu kan lamarin ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.