Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
‘Yan damfara na cutar da mutane ta waya

‘Yan damfara na cutar da mutane ta waya

Wasu batagari cikin al’umma suna nan suna yaudarar mutane ta hanyar kiransu ta wayar tafi-da-gidanka. Wasu sukan nemi bayanin mutum kafin su kira shi, domin su san ta yadda za su bullo masa, wasu kuma na samun lambar mutum ne da sunansa sai su kira su jarraba sa’a, amma ba da sanin cikakken bayani game da shi ba. Sukan bi hanyoyi da dama na yin yaudara a lokacin da suka kira mutum a waya. ga wasu kadan daga cikin hanyoyin: Za su kira waya tare da canza murya wanda mutum zai yi tunanin ba muryar dan Adam ba ce wadda ya saba ji yau da kullum ba. Wasu suna nuna cewa su jinsi ne na JINNU, ko kuma RAUHANI.  
Da farko za su kira mutum tare da ambaton sunansa kai tsaye, kai ka ce mutumin da kuka dauki tsawon shekaru ne wanda ya dade da sanin ka, su kan ce wa mutum ya samu wani abu ya yi sadaka da shi ko ya yi kyauta. Misali, za su ce ka nemi fararen goro kamar guda uku ka yi sadaka ko kuma dabino, ko su ce maka ka fanshi Alkur’ani ka kai masallaci, idan ka yi wannan abin da suka umurceka da shi, za su ce ka sake kiransu domin su taimaka maka, inda za su yi maka addu’a. A cikin jawabinsu na yaudara sukan rika sako ayoyin Alkur’ani da hadisan Manzon Allah (SAW) duk don dai mutum ya yi amanna ya yarda da su, sai su ce wa mutum ya zabi bukatu kamar guda uku  zuwa hudu, wadanda yake da su a nan duniya, su kuma za su yi masa rokon Allah a kai.  Wai a cewarsu za su sanya almajiransu su yi saukar Alkur’ani, wanda daga nan ne za su fara kawo bukatun su na damfara, bayan sun gargadeka da kada ka bayyana wa kowa surrinka. Sukan bukaci cewa, sun yi wa mutum saukar Alkur’ani to za a yi yankan rago. Don haka sai mutum ya fadi adadin kudin ragon da zai iya saye, daga nan sai su umurci mutum ya tura musu kudin ta hanyar sayen kati tare da kankare shi a tura masu lambobin katin, wai za su sayar domin su ne za su sa yi ragon a wurin su, su yi wa mutum amfani da shi.
Idan ka ce su ba ka Lambar Asusun Ajiyar Banki (Account No.) don ka tura masu kudin, za su ce, su ba sa amfani da wannan, domin suna tunanin asirinsu na iya tonuwa. Kuskuren tura musu abin da suka bukata, ta hanyar katunan waya zai sa ba za ka kara samun su ta wayar ba, ko kuma ko da ka same su ba za su kara daga wayar mutum ba.
Wata hanyar kuma ita ce mutane  sukan yi hadin baki kamar su uku. Mutum na farko zai kira tare da nuna ya sanka, bayan nan zai nuna maka cewa wani alheri ne ya zo da shi, amma shi ba ya kusa don haka zai hada ka da mutanen da za a yi wannan hulda da su. Zai turo maka lambobi na sauran mutum na biyu da na uku, zai ce ka kira su. Idan ka kira mutum na biyu zai nuna maka cewa, wasu kaya ne suke so a kawo musu,  misali kayan kamfani, kuma zai bayar da farashi mai kauri, wanda hakan zai sa mutum ya rude domin yana ganin zai samu wata riba mai kauri a cikin kankanin lokaci. Amma su masu sayen kayan za su ce maka sai ka zo musu da samfur na irin kayan.  Hakan zai sa mutum ya yi gaggawar kiran mutum na ukku, wanda zai kira kansa manajan kamfani na kayayyakin da aka baka oda. bayan ka tambaye shi irin kayan da kake so zai cemaka akwai, idan ka bukaci za ka je ka same shi domin ku yi magana don ka karbi samfur, zai nuna maka cewa dokar kamfani bai yarda da a fita da kaya ba sai anyi da fositin wasu kudi. don haka idan kana son samfur na kaya to za su iya turo maka  lambar asusun ajiya a banki, ka sa wasu kudi kamar na ajiya, bayan ka saka sai ka je musu da takardar shigar da kudi banki (bank tellar) kafin su baka Samfur. A daidai wannan lokaci mutum na biyu masu sayen kaya za su kira ka tare da nuna wani wuri da suka sauka. Misali za su ce suna wani otal da ke garin da mutum yake, don haka ka zo ka karbi kudi ka kawo musu kaya, amma fa sai ka zo da samfur tukuna.  Kila kudin da suka bukata mutum ba ya da su.
Don haka mutum zai yi tunanin bari ya kira mutumin nan na farko, tare da tambayar sa mafita, shi kuma a lokacin zai nuna maka cewa a inda yake babu yadda za a yi ya iya turo kudi, amma ko da rance ne mutum ya je ya samo a tura musu, domin a karbo wannan samfur. zai nuna wa mutum yawan ribar da za a samu duk ta hanyar yaudara. Wanda daga  karshe idan mutum  ya tura wadannan kudi to za a bar shi da takardar banki wato tela.
Ya kamata duk sa’adda mutum ya samu kiran irin wadannan miyagun mutane to ya yi kokarin kai rahoto da wuri-wuri ga hukuma, ita hukuma na iya kokarin bin sawun wadannan miyagun mutane ta lambar wayar da suke kira da ita, ko ta lambar asusun ajiyar da suke turowa don a tura musu kudi.
Hakan zai yiwu ne tare da taimakon kamfanin samar da layukan wayar salula da kuma ma’aikatan bankuna. Shi ya sa muke jawo hankalin irin wadannan mutane mayaudara da su ji tsoron Allah, su tuba su daina. Sauran jama’a kuma mu rika yin takatsantsan a duk lokacin da muka samu kiran wani ko wata, a jerin mutanen da ba mu san su ba, wai da niyyar suna son su taimaka mana. Saboda kada ‘garin neman kiba a samo rama!. Allah ya kara tsaremu da tsarewar sa ameen.
Habibu Ibrahim ya rubuto makalarsa ne daga Central Market Katsina  07038653949 habibuibrahim@gmail.com