✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi masu sanya kayan soja sun shiga hannu a Legas

Asirin wadansu da ake zargin ’yan fashi da makami ne da suke sanya kayan soja suna tsare hanyar nan ta Mowe a Jihar Ogun, suna…

Asirin wadansu da ake zargin ’yan fashi da makami ne da suke sanya kayan soja suna tsare hanyar nan ta Mowe a Jihar Ogun, suna yi wa jama’a fashi ya tuno, bayan da ’yan sandan jihar suka kama daya daga cikinsu.

A cewar Kakakin Hukumar ’Yan sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, dubun ’yan fashin ta cika ne bayan da suka yi wa wani tsohon soja fashin Naira dubu 86 a ranar 13 ga watan jiya; lamarin da ya sa ya yi kararsu a ofishin ’yan sanda na yankin.Babban Jami’in ’Yan sandan yankin, CSP Francis Ebuhoma ya jagoranci kai wa ’yan fashin samame, inda suka yi nasarar kama daya daga cikinsu mai suna Adeoye Ayomide. Wanda aka kaman, dan shekara 23, yana sanye da kayan soja.

Farancis ya ce bayan da ’yan sandan suka yi bincike a gidan wanda ake zargin dan fashi ne, sun gano karin kayan soja da suke sanyawa suna fashi da su.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Ahmad Iliyasu ya ba da umarnin a mika wanda ake zargi ga sashin Yaki da Miyagun Laifuffuka da Fashi da Makami (FSARS), kuma ya ba da umarnin a kamo ragowar ’yan fashin.