✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwa sun koka a kan sabon tsarin fitar da kudi a bankuna

Binciken da Aminiya ta gudanar a Abuja da Kano ta gano sabon tsarin fitar da kudi da Babban Bankin Najeriya ya kirkiro wanda ya kunshi…

Binciken da Aminiya ta gudanar a Abuja da Kano ta gano sabon tsarin fitar da kudi da Babban Bankin Najeriya ya kirkiro wanda ya kunshi bankuna za su rika cire haraji ga kwastomominsu idan za su cire kudi ko kuma ajiye ya jawo wa ‘yan kasuwa asara.
An fara amfani da wannan sabon tsarin ne a Legas a watan Janairu, 2012, daga baya kuma jihohi biyar suka bi sahu a watan Yuli, 2012. Jihohin sun hada da Kano da Ribas da Anambra da Ogun da Abiya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Sabon tsarin ya umarci bankuna su rika cire harajin kashi 2 cikin 100 na duk wani kudi da za a cire ko za a adana da ya kai Naira dubu 500 ga kowane mutum. Haka za a cire kashi 3 cikin 100 na kudin da ya kai miliyan 3 ga asusun hadin-gwiwa na kungiyoyi ko kamfanoni da sauransu.
Haka kuma tsarin ya umarci bankuna su cire harajin kashi 2 cikin 100 ga duk mutumin da zai cire Naira dubu 500 a kan kanta. Ga kamfanoni ko kungiyoyin da za su cire Naira miliyan 3 a kan kanta kuma za a cire musu harajin kashin 5 cikin 100 na kudin da za su cire din.
’Yan kasuwa da kungiyoyi da sauran jama’a sun bayyana asarar da suka yi makonni biyu da fara wannan sabon tsarin a Abuja da kuma Kano.
Tun da aka fara sabon tsarin bankuna suke shan daga da kwastomominsu wajen yin amfani da tsarin, inda da yawa daga cikin ‘yan kasuwa suke korafi hade da barazanar za su daina kai  ajiya bankuna. Wannan sa-toka-sa-katsin da ya cukwiykuye sabon tsarin ne ya sanya Babban Bankin Najeriya ya daga kafa wajen ci gaba da sabon tsarin zuwa 2 ga watan Oktoba.
Sai dai tun bayan da aka ci gaba da amfanin sabon tsarin ne ‘yan kasuwa suka ci gaba da korafi, inda suke cewa sabon tsarin ya zama wata barazana ta hallaka ribar da suke samu, wanda hakan zai zama sila ta karayar jarinsu, a karshe maimaikon tsarin ya sanya kwalliya ta biya kudin sabulu, sai dai ya zama a garin gyaran gira sai a rasa idanu.
Wakilinmu sun ji ta bakin ‘yan kasuwa a Abuja da Kano inda suka bayyana ra’ayinsu, inda suka ce tsarin ba zai haifar da da mai ido ba, kuma hakan zai rage wa mutane samun kwarin gwiwa wajen ci gaba da kai wa ajiya bankuna.
A daya daga cikin bankuna ne wakilinmu ya ji wani dan kasuwa na korafin an cire masa harajin dubu 36 a lokacin da ya ajiye kudi a asusunsa.
“Ban taba ganin al’amari irin wannan ba. Babu adalci a ciki. Zan tuna lokacin da kake (ma’aikacin bankin) rokonmu don mu rika hulda da bankinku. Amma da yake yanzu bukatarku ta biya wurin tara kwastomomi sai ga shi kun kirkiro wani tsari da zai kore mu. Ba za mu yarda da wannan ba. Ribar da muke samu ba ta taka-kara ba, ballantana har mu ci gaba da tsayawa da kafafunmu bayan an ci gaba da cire mana harajin.” Inji dan kasuwar.
Aminiya ta gano ‘yan kasuwa da ke hulda da wurin canjin kudi da kuma diloli a masaku da ke kasuwar Kantin Kwari, a Kano da masu sayar da kayan abinci da ‘yan kasuwar Kasuwar Singer a Kano sun ce suna shan matukar wahala wajen bin wannan sabon tsarin.
Adamu Abdullahi (ba sunansa da asali ba) mai sayar da shinkafa ya ce dole ta sanya ya guje wa sabon tsarin bayan ya kammala cin kasuwa sai ya kai kudinsa gida.
Ya ce: “Yawancin kwastomominmu suna amfani da kudi ne ba cek, sukan yi mana korafin dogayen layuka a bankuna idan mu bukaci sun rika sanya mana kudi a asusunmu. Don haka ba mu da wata mafita face mu karbi kudin idan sun kawo mana, hakan ya sanya muke kai wa kudin bankuna da kanmu. Amma a halin da ake ciki sakamakon sabon tsarin da aka kirkiro babu wanda yake so ya kai makudan kudi banki a rana daya, inda harajin yake yi wa ribar da muke samu kafar ungulu.”
“A yanzu ’yan kasuwa da dama sun koma tsohon tsarin ajiyar kudi a gida mai cike da hadari inda suke ajiye kudi a gidajensu. Don haka ya kamata Babban Banki Najeriya ya sake lale da kuma tunani musamman ma ya yi la’akari da matsalar tsaro. Ba za mu ci gaba da ajiye kudi a gida ba.” Inji shi.
A Abuja wannan tsarin ya haifar da cece-kuce inda wasu suka yi lale-marhabin da shi, wadansu kuma kokawa suka yi, inda suka ce hakan zai kawo tsaiko a harkar kasuwanci.
Wakilinmu ya tattauna da wadansu masu matsakaita da kananan masana’antu (SMEs) a Abuja a kan wannan sabon tsari da Babban Bankin Najeriya ya ce babu gudu babu ja da baya.
Nasir Muhammed, wani mai kamfanin African Clothing da ke Kasuwar Utako ya yaba wa sabon tsarin sai dai ya ce da yawa daga cikin ‘yan kasuwa ba su da ilimin yadda tsarin yake musamman ma wadanda ba su yi makaranta ba.
“Da yawa daga cikin mutane kawai sukan dauki kudinsu su sayi abubuwan da suke so ne ba tare da ba banki damar yin ruwa da tsakin cikin al’amarin ba, a ganinsu hakan bata lokaci ne.” Inji Nasir.
Ya ce, duk da cewar bai fara sabon tsarin ba don haka bai san yadda harajin yake ba, amma dai shi ya saba karbar kudi ne a duk lokacin da ya gudanar da kasuwanci ba wai a yi harkar banki ba.
A karshe ya nemi a kara wayar da kan jama’a dangane da amfanin sabon tsarin, “ya kamata gwamnati ta tashi tsaye wajen wayar da kan jama’a don su fahimci amfani sabon tsarin. Idan an yi hakan na tabbata jama’a za su ba da hadin kai. Babbar matsalar ita ce da yawa daga cikin ‘yan kasuwa ba su fahimci ta yadda tsarin zai amfane su ba.”
Popoola Olajumoke mai sayar da kifi da ke kasuwar kifi ta Kado ta ce ba ta yi murnar zuwan sabon tsarin ba saboda harajin ya yi wa duk mai sana’a irin tata yawa.
“Wani lokaci idan muka yi ciniki mai yawa za mu bukaci ajiye kudi a banki, saboda haraji ai ba za ka ce za ka rarraba kudi a bankuna ba, wani lokaci rabe-raben kudin a bankunan ma yakan sanya kowacce ajiya a cire wa  mutum harajin 1,500. Don haka harajin da za a cire na kashi 3 cikin 100 na ajiya ko cire Naira dubu 500 ba ubansu ba ne.” Inji ta.
Babson Bartholomew mai shagon sayar da littattafai ya ce ya yi maraba da sabon tsarin, sai dai wani lokaci akan samu tsaiko amma nan da wani lokaci jama’a za su saba da shi. “Ina son wannan tsari saboda yana saukaka harkar kasuwanci. Har yanzu ba a cire mini harajin ba saboda na takaita yadda nake cire kudi. A ganina ba za a samu matsala a manyan birane ba saboda an saba da irin wannan harkar, sai dai a karkara ne za a samu matsala saboda mutanen can ba su saba da hakan ba, kuma zai dauki lokaci.
Ya shawarci a magance matsalar intanet da ake samu a bankuna da take kawo tsaiko, idan an yi hakan jama’a ba za su rika korafi ba.
Tsarin ‘pilot scheme of moblie’ wani tsari ne na amfani da wayar salula da Babban Bankin Najeriya ya kawo wajen saukaka harkar kasuwanci don a bunkasa tattalin arziki. An shirya tsarin ne da ‘yan kasuwa za su rika amfani da wayoyinsu wurin  gudanar da harkokin kasuwancinsu a birane da kauyuka.