✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Kasuwar Kafanchan sun yaba wa SEMA kan tallafi

Kungiyar ’Yan Kasuwar Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna ta yaba wa Gwamnan Jihar Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i da Hukumar Bayar da…

Kungiyar ’Yan Kasuwar Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna ta yaba wa Gwamnan Jihar Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) kan gudunmawar da suka bai wa ’yan kasuwar da gobara ta cinye wa shaguna da kayayyaki a farkon shekarar nan.

Da yake bayani jim kadan da karbar gudunmawar, Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa ta Karamar Hukumar Jama’a, Alhaji Salisu Idris ya ce tallafin ya zo a daidai lokacin da ’yan kasuwar ke bukata lura da halin da ake ciki.

“Tun bayan faruwar lamarin muka rubuta wa gwamnati kan bukatar tallafa wa ’yan kasuwar ga shi bayan wata shida sun ba mu tallafin buhunan siminti da kwanukan rufi,” inji shi.

Shugaban ya jinjina wa Shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Mista Peter Aberik da Kansilan Kafanchan “B” Zakariya’u  Bala wanda bisa kokarinsu ne Allah Ya taimaka gwamnatin jihar da Hukumar SEMA suka waiwaye su.

Tunda farko da yake kaddamar da mika gudunmawar, Kansilan Kafanchan ‘B’ kuma Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Karamar Hukumar Jama’a Malam Zakariya’u Bala, bayan jajanta wa ’yan kasuwar, ya yi kira gare su musamman masu sana’a ko amfani da wutar lantarki su rika kiyayewa tare da tabbatar da sun karkashe na’urorinsu kafin su kulle shagunansu bayan sun tashi daga kasuwar.