✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwar Nijar za su hada gwiwa da na Najeriya don bundasa kasuwanci

Matasa ‘yan kasuwar jamhuriyar Nijar za su hada gwiwa da takwarorinsu na Najeriya domin dara bundasa harkokin kasuwanci a tsakanin dasashen biyu. Shugaban dungiyar matasa…

Matasa ‘yan kasuwar jamhuriyar Nijar za su hada gwiwa da takwarorinsu na Najeriya domin dara bundasa harkokin kasuwanci a tsakanin dasashen biyu.
Shugaban dungiyar matasa ‘yan kasuwa na dasar Nijar  Muhammad Alhaji Sule danfeti Damagaram  ne ya bayyana wa Aminiya haka a yayin da take zantawa da shi.
Shugaban ya ce sun kafa wannan dungiya ce da nufin kawo sauyi da cigaban kasuwanci a dasar Nijar ta hanyar tallafa wa juna musamman a kan abin da ya shafi fadawar wata daddara ga dan kasuwa da bayar da tallafin jindai da rance tare da tsaya wa abokin kasuwanci.
Muhammad ya ci gaba da cewa,kasancewar Najeriya babbar abokiyar kasuwanci ya sa ya zama wajibi da su nemi hadin gwiwa da ‘yan kasuwarta domin daidaita gidin da ake samu a harkokin kasuwanci. “Idan aka lura ana samun matsalar rashin amincewa a tsakanin juna a dukkan dasashen ta hanyar yaudara ko cin amana da sauran irinsu,ke nan shigowar dungiya a tsakiya za a samu saudin faruwar haka”.inji danfeti.
 Shugaban dungiyar  ‘yan kasuwa matasan sai ya nuna takaicinsa a kan irin yadda ake barin dasashen Afirika a baya ta fuskar kasuwanci duk da irin arzikin da Allah Ya yi wa yankin, amma maimakonmutanen da ke yankin su amfana sai wadansu daga waje suke amfana da su. ‘’Har ila yau babu taimakon juna a tsakaninmu balle kuma tunanin kafa wadansu kamfunna don hadaka harkokin kasuwanci, wadannan suna daga cikin nadasun da ake samu, bama kamar ga matasa.’’
“Ina kira ga ‘yan uwanmu ‘yan kasuwar Najeriya da su zo mu hada hannu da darfi da darfe don ganin cewa mun kawo sauyi a harkokin kasuwanci. Nan bada dadewa ba za mu kawo ziyara ga dungiyoyin ‘yan kasuwa, musamman matasa, domin kusan sune a yanzu suke tafiyar da al’amurran kasuwanci a duniya ma baki daya. Muna kira ga manyan ‘yan kasuwa iyayenmu da a kowane lokaci su rida sanya mu a kan hanya a duk inda suka ga mun kauce.”inji danfeti.