Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Yan Majalisar Kano sun kammala karatu na biyu don kirkiro da masarautu 4

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi wa kudurin dokar kirkiro sabbin masarautu hudu a jihar, a yau aka yi karatu na biyu.

‘Yan majalisar dai sun dage zaman da suke yi, inda suka shiga wani zaman sirri. Sa’annan bayan zaman sirrin, ake saran za su yi wa kudurin dokar karatu na uku, kuma daga nan sai amince da kudurin ya zama doka.

ADVERTISEMENT

A daya varayin kuma, an ruwaito gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, yana mai alwashin amincewa da dokar, da zarar ‘yan majalisar sun kammala amincewar kudurin dokar.

ADVERTISEMENT