Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Yan majalisar Kano sun mika dokar kirkiro masarautu 4

‘Yan majalisar dokokin jihar Kano sun mika kudirin dokar kirkiro da sabbin masarautu hudu a jihar wadanda suka hada da: Gaya, Bichi, Karaye da Rano

Kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ne ya jagoranci muhawarar da ‘yan majalisar suka yi, bayan kwamitin da aka kaddamar  sun amince da kudirin dokar kirkiro da sabbin masarautu.

ADVERTISEMENT

A yanzu haka zauren majalisar za su mika kudirin dokar ga Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje rattaba hannu.

ADVERTISEMENT