✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya sun gaji da bakin mulkin PDP – Jarman Kebbi

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kabi kuma Sakataren Tsare-Tsare na kasa na Jam’iyyar ANPP, Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu Jarman Kabi, ya ce ’yan Najeriya sun gaji…

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kabi kuma Sakataren Tsare-Tsare na kasa na Jam’iyyar ANPP, Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu Jarman Kabi, ya ce ’yan Najeriya sun gaji da bakin mulkin Jam’iyyar PDP da take rika da ragamar wannan kasa daga 1999 zuwa yau.
Alhaji Sulaiman Argungu ya bayyana haka ne ga manema labarai a Birnin Kebbi, inda ya ce al’ummar kasar nan ba su gamsu da yadda PDP ke gudanar da al’amura da dama ba, balle su yi alfahari da ita ba. Ya ce idan aka lura da irin tururuwan da jama’a suka yi zuwa tarurrukan da jam’iyyun adawa suka yi ya nuna an gaji da mulkin Jam’iyyar PDP.
Ya nanata kudarin shugabannin Jam’iyyar ANPP a kasa na shiga sabuwar Jam’iyyar APC da ’yan Najeriya ke muradi don magance matsalolin da suke addabar ’yan Najeriya.