✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan PDP sun yi zanga-zanga a ofishin Amurka da Birtaniya a Abuja

Shugabannin jam’iyyar adawa ta PDP tare da mambobin jam’iyyar sun gudanar zanga-zangar lumana saboda zargin jam’iyyar APC da rashin tabuka komai a kan matsalolin da…

Shugabannin jam’iyyar adawa ta PDP tare da mambobin jam’iyyar sun gudanar zanga-zangar lumana saboda zargin jam’iyyar APC da rashin tabuka komai a kan matsalolin da kasar ke fuskanta.

Shugaban PDP na kasa Uche Secondus, da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Peter Obi a zaben 2019, ne suka jagorancin zanga-zangar lumana, zuwa ofishin jakadancin Birtaniya da na Amurka da ke Abuja inda suka mika takardar kokensu.

Shugabannin PDP sun bukaci a yi adalci a hukuncin kotun koli wajen karbe kujerar Gwamnan Imo na PDP Emeka Ihedioha, aka bai wa dan takarar Gwamnan APC.