Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
’Yan sanda bakwai sun mutu a hatsarin mota

’Yan sanda bakwai sun mutu a hatsarin mota

Akalla ’yan sanda bakwai ne suka mutu a wani hadarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a daidai barikin sojoji na Jaji.

‘Yan sandan na cikin farar bus ce mai daukar mutum 18 sai dai babu wanda ya san abin da ya janyo hadarin.

“Mu dai mun zo lokacin da motar ta kife da ’yan sandan kuma na kirga gawarwaki kusan ’yan sanda bakwai, sannan biyu na kwance cikin jini wasu kuma sun tsallake babu rauni,” inji wani direba mai suna Hassan.

Aminiya ta ruwaito cewa, babu wanda ya san inda ’yan sandan za su ko suka fito amma suna sanye da kayansu kuma rike da makamai.

Kakakin rundunar na jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige ya ce sun tura jami’an ’yan sanda wurin da hatsarin ya faru domin tabbatar da abin da ya faru.