✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama aku saboda ankarar da masu fataucin kwaya

An tsare wani aku da ya ankarar da wadansu masu kwangilar fataucin kwayoyi a Brazil su biyu. Ana zargin akun cewa ya sanar da mutanen…

An tsare wani aku da ya ankarar da wadansu masu kwangilar fataucin kwayoyi a Brazil su biyu. Ana zargin akun cewa ya sanar da mutanen ne cewa, ga ’yan sanda suna zuwa maboyarsu da suke adana miyagun kwayoyin.  ’Yan sanda sun tsare akun ne a gidan wanda ya mallake shi a garin Teresina  da ke kasar Brazil kamar yadda kafar labarai ta Oliberal.com ta ruwaito.

Duk da yunkurin akun wajen sanar wa masu safarar miyagun kwayoyin bai hana tona asirin wadanda ake zargi da mu’amala da miyagun kwayoyin ba. An samu miyagun kwayoyin da suka hada da Hodar Iblis da tabar wiwi da kudade masu dimbin yawa a moboyar tasu.

’Yan sandan ba su sanar da sunan akun da aka kama ba, wanda har yanzu ke ci gaba da biyayya ga wanda ya malleke shi, kuma ya ki rera wakar da ya saba yi irin ta kanari. Jaridar ‘The Guardian’  ta wallafa cewa, akun da aka tsare ya ki yin magana da ’yan sanda kuma ya ki furta irin sautin da ya saba yi.

Hukumomi sun fahimci cewa, an horar da akun kan yadda zai lura da motocin ’yan sanda, kuma a yanzu haka an ajiye akun a gidan adana  dabbobi da tsuntsaye na birnin Teresina da ke Arewa maso Gabas na Brazil, kamar yadda kafar labarai ta Oliberal.com ta sanar.