✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama makiyaya 3 da ake zargi da kashe manomi a Ogun

Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta kama wadansu Fulani makiyaya uku da ake zargi da kashe wani manomi mai suna  Rafiu Sowemimo a kauyen Alabata…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta kama wadansu Fulani makiyaya uku da ake zargi da kashe wani manomi mai suna  Rafiu Sowemimo a kauyen Alabata da ke jihar.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ta kama Fulani makiyayan wadanda suka hada da Muhammed Adamu da  Salisu Ismail da kuma Salihu Adamu, ya ce gardama ce ta kaure a tsakaninsu da manomin lokacin da suka shiga gonarsa da dabobbinsu inda ya yi musu magana sai suka sassare shi lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar manomin mai shekara  40.

Ya ce mutanen kauyen Alabata ne suka ankarar da ’yan sanda cewa wadansu Fulani makiyaya sun shiga gonar marigayin, kuma  lokacin da ya tare su domin ya ji dalilinnsu na yin haka sai suka daba masa wuka suka sassare shi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun Alhaji Bashir Makama ya ziyarci iyalan marigayin inda ya jajanta musu ya kuma ba da umarnin a tura wadanda ake zargin zuwa sashen bincikar manyan laifuffuka na rundunar domin zurfafa bincike.