✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun yi awon gaba da Basarake kan fadan kungiyar asiri

Tawagar wasu jami’an tsaro ’yan sanda da ke  aiki sashen dakile fashi da makami wato SARS sun taho tun daga Abuja, ba su zame ko’ina…

Tawagar wasu jami’an tsaro ’yan sanda da ke  aiki sashen dakile fashi da makami wato SARS sun taho tun daga Abuja, ba su zame ko’ina ba sai fadar Sarkin Ugep Hedkwatar karamar Hukuar Yakurr a Jihar Kuros Riba, inda suka yi awon gaba da Basaraken garin wato  Obol Ofem Ubana.

Bayanai da wannan jarida ta samu daga garin Ugep na nuni da cewa da misalin karfe sha biyu na ranar Talata da ta gabata ne ’yan sandan SARS daga Abuja suka yi tsinke ba su zame  ko’ina ba sai fadar Basaraken  Obol Ofem Ubana suka kama shi, suka tafi da shi Abuja.Wata majiya da ke rundunar ‘yan sandan Jihar Kuros Riba ta shaida wa wakilinmu cewa, ‘ba a tafi da shi Abuja ba, amma yana hannunsu.’

Bayanai masu tushe daga garin Ugep da suka yi wa  Aminiya sun nuna  cewa kama Basaraken na da nasaba da fadan ’yan kungiyar asiri da matasan Ugep suka yi ne kwanan baya, wanda sanadin haka aka kashe dan yayan babban jami’in gwamnatin  mai bai wa shugaban kasa shawara kan matakan shari’a, kuma matashin da ya yi kisan an ya shiga hannu, inda ya tsere  zuwa Jihar Akwa Ibom. 

Kwanan baya mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin shari’a Barista  Okoi Obono-Obla, aka ce ya rubuta takardar koke wadda ya aika wa shugaban kasa yana neman a bi masa kadin wadanda suka kashe  dan wansa Jude Iroegbu,  a fadan kungiyar asiri ta bikins da Black Ade  suka yi a garin.

Aminiya ta tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kuros Riba Irene Ugbo, game da kama Basaraken ta tabbatar da kama shi ta ce yana da hannu, kuma ana zarginsa ne da yin watsi da fadan da ’yan kungiyar asiri suke yi ne a garinsa ba tare da kulawa ba.