✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sandan da suka harbe mutum a gidan rawa sun shiga hannu

“Yan sandan da suka harbe wani matashi a gidan rawa na Kires Inn da ke Unguwar Balogun Karamar Hukumar Oshodi ta Jihar Legas sun shiga…

“Yan sandan da suka harbe wani matashi a gidan rawa na Kires Inn da ke Unguwar Balogun Karamar Hukumar Oshodi ta Jihar Legas sun shiga hannu bayan da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Hakeem Odumosu ya ba da umarnin kama su.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Legas, DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ya ce ’yan sandan sun yi harbin kan mai uwa da wabi ne a gidan rawar da misalin karfe 8:30 na dare, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wani matashi mai shekara 27 mai suna Maliki Muhammad yayin da wadansu mutum biyu suka jikkata.

Ya ce ’yan sandan da ake zargi da hannu a lamarin sun hada da Sufeta Orubu Olusola da Sufeta Apalowo Ola da sai Sufeta Kasai Sule da Saje Momoh Ogwuche da Saje Adoga Collins, kuma suna aiki ne a ofishin rundunar da ke shiyyar Akinpelu kuma a lokacin suna karkashin kulawar  baturen ’yan sandan da ke kula da sashen laifuffuka na shiyyar DSP Oloko Wale da ASP Adamu Babajo, baturen ’yan sanda mai kula da sashin ayyuka na shiyyar.

“A jawaban da suka gabatar ’yan sandan da ake zargin sun ce, sun je gidan rawar ne bayan da wata mace mai suna Makude Omowunmi Aminat ta shigar da koke cewa, an ci zarafinta a gidan rawar, sun je domin su kama wadanda suka ci zarafin matar sai gugun batagari suka rufar musu lamarin da ya sanya su yin harbi domin kare kansu. Yanzu haka ana bincike a sashen bincike da ladabtarwa na rundunar kuma da zarar an same su da laifi za a gabatar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukunci kuma za a ci gaba da bayyana wa al’umma halin da ake ciki,” inji DSP Elkana.

Ya ce, ya aike da takardar sammaci ga ’yan sanda uku da ke kula da ’yan sandan da ake zargi bisa tuhumarsu da yin sakaci wajen kula da ’yan sandan da ake zargin.

Ya ce an kuma kama mutum 11 da ake zargi da far wa ’yan sandan lokacin da suka je gidan rawar.

“Kwamishinan ’Yan sandan ya jajanta wa iyayen wanda ya rasu a lamarin tare da bai wa jama’a tabbacin za a hukunta duk wanda aka samu da laifi, don haka ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu,” inji shi.