✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sandan Kuros Riba sun kama wadanda ake zargi da sace mutum

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Ribas ta gabatar wa manema labarai wadansu mutum hudu ciki har da jami’in tsaro na farin kaya (DSS) da ake…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Ribas ta gabatar wa manema labarai wadansu mutum hudu ciki har da jami’in tsaro na farin kaya (DSS) da ake zargi da sace wani mutum. Wadanda aka gabatar su ne: Wata mai shekara 26 mai suna Sylbia James da  Eyo Edet Okon, mai shekara 29 da Jason Udo, mai shekara 36 sai Eyo Bassey, mai shekara  31.                                                                                                                                                  Da take karin bayani mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba, Irene Ugbo, ta ce wani mutum mai suna Ogar Bassey ne ya je ofishin rundunar da ke Uwanse a Kalaba ya ce, wadansu mutum biyu da ba a san ko su wane ne ba sun zo gidansu suka kama kannnensa biyu Isaac Sampson mai shekara 21 da Brown Irek Ofadim suka tafi da su wani wuri da ba su sani ba .

Ta ci gaba da cewa duk da kasancewa an yi hikima wajen bincike da kuma gano inda aka kai wadanda aka kama din, an dai gane su a wata unguwa ce mai suna Atimbo inda aka kamo wadanda ake zargin a wata mota kirar Toyota Camry mai lamba CAL 237 CG sannan an kama su da wata sharbebiyar wuka da wayoyin hannu.

Irene, ta ce jami’in DSS din da ake zargi da hannu a aikata laifin kama mutane a yi garkuwa da su “Mun rubuta wa ofishinsu wasika ta neman cikakken bayani game da shi ko ma’aikacinsu ne ko a’a.

Ana zargin mutanen ne da zuwa  gidan wani mai suna  Robert Bassey, suka kama shi suka yi garkuwa da su suka nemi a ba su kudin fansa Naira dubu 250 idan kuma ba a ba su ba, su  kashe su.

Eyo Edet Okon daya daga cikin wadanda ake zargin ya shaida wa Aminiya cewa, “Karya ne ba garkuwa muka yi da shi ba,  mun je gidan Robert Bassey ne domin mu karbi kudinmu Naira dubu 107  daga hannunsa. Kuma ya  karbi Naira dubu 48 daga hannun kanwata, mun sha zuwa gidansa  kan ya ba mu kudinmu da ya amsa da nufin samar mana da gurbin shiga Jami’ar Kalaba amma ba kudinmu babu kuma makarantar.”

Ya ce: “Ganin kudinmu  sun makale ne babu yadda za a yi su fita ya sa muka yanke shawarar sanarwa abokinmu jami’in DSS domin ya sanya baki ya biya mu kudinmu. Ganin mun yi ta zuwa domin karbar kudin ana ce mana baya nan, domin ya fito daga duk inda ya boye ya sa aka kama kannensa biyu aka tafi dasu ofishin DSS, domin ya bayyana ya yi bayanin yadda kudinmu za su fito. Daga baya, bayan DSS sun yi bincike kan kudin sai suka ce wadancan kannen Robert su koma gida su kuma ’yan sanda sai suka juya magana suka ce mu masu kama mutane ne muna yin garkuwa da su don neman kudin fansa alhalin ba haka ba ne.”