Da Dumi Dumi

Yanzu PDP ta farfado  Karamar Hukumar Lere – Lawal Rabi’u

Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u

Dan Majalisar Wakilai daga mazabar Lere a Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u da aka rantsar a makon jiya, ya ce nasarar da ya samu kamar sake farfadowar jam’iyyar ce a karamar hukumar.

Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga dubban mutanen da suka tarbe shi a ranar Asabar da ta gabata a garin Saminaka.

Alhaji Lawal Rabi’u an rantsar da shi ne, bayan da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe da Kotun Daukaka Kara sun tabbatar da cewa shi ya kamata a ba kujerar ba Injiniya Sulaiman Aliyu Lere na Jam’iyyar APC ba.

Ya ce, babu abin da zai  ce ga al’ummar Karamar Hukumar Lere, kan wannan tarba da suka yi masa, sai  dai godiya. Ya ce ya so ya zo tun nasarar da aka fara samu a kotu ta farko da kotu ta biyu, amma haka ba ta yiwu ba, har sai da aka rantsar da shi.

“Lokacin da aka tabbatar da nasarata, na je ne in ga Shugaban Majalisar Wakilai, don ya ba ni ranar da za a rantsar da ni. Nan take ya ce a rantsar da ni a lokacin, dalilin da ya sanya ke nan ba mu sanar da jama’a kan ranar da za a rantsar da ni ba,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Alhaji Lawal Rabi’u ya bada tabbacin cewa, za su ci gaba da yin abubuwan da za su taimaki al’ummar karamar hukumar.

Ya mika  godiy  ga dukkan wadanda suka bada gudunmawa kan wannan nasara da suka samu.

A jawabin tsohon dan Majalisar Wakalai na mazabar Lere Alhaji Ibrahim Lawal Nuhu Kayarda ya mika godayarsa ga al’ummar karamar hukumar, kan goyon bayan da suka ba Jam’iyyar PDP,  har aka kai ga samun nasara.

“A yanzu  wannan dan Majalisar  Tarayya shi kadai  PDP ke da shi a Shiyya ta Daya a Jihar Kaduna. Saboda haka muna bukatar a ci gaba da ba mu goyon baya da shawarwari, domin ya kawo mana ci gaba a wannan karamar hukuma,” inji shi.

Tun farko a jawabin Shugaban Jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar Lere, Alhaji Tasi’u Bala  ya ce wannan nasara da suka samu a Jam’iyyar PDP, kamar an yi musu allura ce. Ya ce yanzu jam’iyyar da take mulki a karamar hukumar, ta tabbatar da cewa akwai babban kalubale a gabanta.

Ya ce nan bada dadewa ba, za su shirya gagarumin taro domin kowa ya zo ya fadi, irin nasarorin da PDP ta kawo a karamar hukumar.

 

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya