✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Majalisa Ilhan Omar ta roki gafara kan kalaman kin Isra’ila

Sabuwar ’yar Majalisar Dokokin Amurka ’yar asalin Somaliya da ta yi gudun hijira zuwa kasar, Ilhan Omar ta nemi afuwa kan kalamanta na sukar lamirin…

Sabuwar ’yar Majalisar Dokokin Amurka ’yar asalin Somaliya da ta yi gudun hijira zuwa kasar, Ilhan Omar ta nemi afuwa kan kalamanta na sukar lamirin Yahudawa, lamarin da ya sa ’yan jami’iyyun Republican da Democrats suka hadu suka yi tir da kalaman.

’Yar majalisar wadda ’yar Jam’iyyar Democrats ce da ke wakiltar wata gunduma a Jihar Minnesota ta yi wasu bayanai ne inda take cewa akwai wani rukunin ’yan Isra’ila masu kamun kafa  a Amurka, inda take nufin cewa kungiyar huldar Amurka da Isra’ila tana sayen ’yan majalisar domin ba da goyon bayansu ga kasar Isra’ila.

Ta yi wadannan kalaman ne a wani sakon Tiwita a ranar Asabar, tana mai cewa goyon baya da ’yan majalisar ke bai wa Isra’ila suna yi ne saboda kudin da ke fitowa daga Kungiyar AIPAC mai kare akidojin Yahudawa, inda ta kara da cewa koda yake kungiyar ba ta taimaka wa yakin neman zaben ’yan siyasar Amurka kai-tsaye, amma kuma mambobinta za su iya taimakawa kamar yadda Muryar Amurka ta rawaito.