✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yar takarar majalisa ta shirya gasar kwallon kafa a Karamar Hukumar Zangon Kataf

’Yar takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC a mazabar Zangon Kataf, Misis Maureen Yayock Lekwot ta shirya gasar kwallon kafa don…

’Yar takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC a mazabar Zangon Kataf, Misis Maureen Yayock Lekwot ta shirya gasar kwallon kafa don sada zumunta da kuma karfafa wa jama’ar mazabarta gwiwa.

Misis Maureen, ta bayyana wa Aminiya a filin wasa na Samarun Kataf da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf inda ake gudanar da gasar cewa makasudin shirya gasar shi ne tattaro kan matasan mazabar ba tare da la’akari da kabila ko addini ba, da niyyar su tunkari siyasar da ke tafe da irin wannan ruhin na yin watsi da maganar addini ko kabilanci a harkokin siyasa.

“Kamar yadda matasa daga addinai da kabilu daban-daban suke haduwa waje daya ba tare da bambanci ba, haka nake so matasanmu su tunkari siyasa ba tare da nuna wariyar addini ko kabila ba,” inji ta.

Wasan an shirya shi ne a tsakanin kulob-kulob takwas da suka fito daga mazabar da suka hada da Zonzon da Magamiya da Zaman Dabo da Jankasa da Unguwar Gaya da Gora da Ikulu da garin Zango.