✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yarinya ta dabawa mahaifinta wuka ya mutu a Delta

An tsare wata yarinya ‘yar shekara 14 wanda aka sakaya sunanta da zargin ta kashe mahaifinta ta hanyar daba masa wuka. Hukumar ‘yan sandan jihar…

An tsare wata yarinya ‘yar shekara 14 wanda aka sakaya sunanta da zargin ta kashe mahaifinta ta hanyar daba masa wuka.

Hukumar ‘yan sandan jihar Delta sun tabbbatar da aukuwar lamarin a unguwar Cable Point da ke Asaba babban birnin jihar.

Rahoton dai na nuna cewa, yarinyar ta samu rashin fahimtar juna tsakaninta mahaifin a  yammacin ranar Alhamis, laifin da ‘yar ta yi wa mahaifinta yasa ya yi fushi da ita, yayin da ita kuwa ta jira har zuwa lokacin da mahaifin ya kwanta barci ta daba masa wuka ya mutu.