✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yarjejeniyar zaman lafiya ta ‘yan takara, ba a nan gizo ke sakar ba

A makon jiya ne ’yan takarar shugabancin kasar nan suka sanya hannu a wata yarjejeniya domin tabbatar da an gudanar da yakin neman zabe da kuma…

A makon jiya ne ’yan takarar shugabancin kasar nan suka sanya hannu a wata yarjejeniya domin tabbatar da an gudanar da yakin neman zabe da kuma zabe cikin kwanciyar hankali ba tare hatsaniya ko zubar da jini balle rasa rayuka ba.

Babu shakka wannan yunkuri da wata kungiya ta shirya ya yi daidai, amma wannan za a iya cewa mataki na farko ne kawai, domin kuwa akwai wasu muhimman abubuwa da suka kamata a kula da su domin samun biyan bukata.

Bayan sanya hannu ya kamata a rika ganin ’yan takara suna haduwa da junansu suna gaisawa kuma suna raha a tsakaninsu domin magoya bayansu su rika gani su ma su yi koyi da su yadda ba za su rika daukar hamayya da zafi ba har su rika rikici da abokan adawarsu.

Haka kuma akwai bukatar ’yan takara su rika kula da kalmomin da za su yi amfani da su a yayin yakin neman zabe, walau a kafafen watsa labarai ne ko kuma a yayin da suke kan dandamali. Haka su ma magoya bayansu ya kamata su rika saisaita kalaman da za su yi amfani da su a yayin tallata dan takararsu a duk inda suka samu kansu.

Sannan kuma lallai ya kanata masu amfani da kafafen sada zumunta su rika lura da abubuwan da suke sanyawa, domin wadansu suna zama ne su kirkiri karya su danganta ta da wani dan takara da nufin bata shi, wanda hakan na iya harzuka wadansu mutane har su tayar da hankalin sauran jama’a.

Su kuma kafafen watsa labarai, musamman mallakar Gwamnatin Tarayya da jihohi, ya kamata su rika yin adalci a tsakanin jam’iyyun siyasa, kada su fifita wata jam’iyya a kan sauran jam’iyyu, domin a shekarun baya wasu gidajen rediyo sun rika nuna bambanci a tsakanin jam’iyya mai ci da kuma sauran jam’iyyun adawa, idan kuma shugaban gidan rediyon ya nemi ya yi adalci sai ya rasa kujerarsa.

Haka kuma wasu kafofin watsa labarai suna bari a yi amfani da su wajen watsa jawaban da za su haifar da fitina saboda dadada wa wata jam’iyya, wanda haka bai dace ba, kamata ya yi duk labarin da kafar watsa labarai za ta watsa ya kasance ta yi adalci ta hanyar tuntubar kowane bangare, wato idan wata jam’iyya ta soki wata, to kafin a watsa a tabbatar an tuntubi jam’iyyar da aka soka domin ta kare kanta daga zargin da aka yi mata. Saboda matukar aka fahimci cewa kafar watsa labarai tana goyon bayan wata jam’iyya hakan zai jawo mata matsala kuma zai iya taimakawa wajen tayar da fitina.

Saboda haka kafafen watsa labarai wadanda suka kunshi rediyo da talabijin da jaridu da kuma uwa uba kafafen sada zumunta, suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a tsakanin ’yan siyasa da kuma a lokacin gudanar da yakin neman zabe. Duk wani abu da aka kawo da suka fahimci zai iya tayar da fitina ko nawa za a biya su ya kamata su yi watsi da shi, kada neman kudi ya sanya su kunna wa kasar nan wuta.

Wata babbar matsala da ke haifar da rikici a lokacin zabe ita ce magudin zabe, inda ake murde  zabe a ce an kayar da wanda ya samu nasara, irin wannan dole ya tayar da hankali, domin zalunci ba ya haifar da alheri.

Su kuma ’yan siyasa ko ’yan takara su guji yin amfani da ’yan banga, ya kamata duk dan takarar da ya yi amfani da ’yan banga a yayin yakin neman zabensa a soke takararsa, domin amfani da ’yan banga da ake yi ne yake haifar da rikici har a kai ga rasa rayuka. Saboda a baya an yi amfani da ’yan banga sosai a harkar siyasa, inda ake amfani da ’yan tauri a yayin yakin neman zabe wanda ya sanya ake yawan asarar rayuka ko nakasa abokan hamayya.

Matasa kuma ya kamata su bar yarda ’yan siyasa suna amfani da su a harkar bangar siyasa suna hallaka kawunansu a banza, alhali su ’yan siyasar ba su bari ’ya’yansu ko ’yan uwansu su shiga irin wannan harka. Duk wanda ya nemi su yi masa aikin banga su ce masa ya kirawo ’ya’yansa su yi tare.

Su kuma shugabannin addini ya kamata su rike matsayinsu na malamai masu shiryar da mabiya su rika yin kyakkyawan aiki, maimaikon tunzura mabiya su rika tayar da hankali, domin yadda wadansu suke maganganu a masallatai ko coci-boci bai dace ba.