✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau za a fara gasar cin kofin Afirka karo na 32

A yau Juma’a ce ake sa ran za a fara fafatawa a gasar cin Kofin Afirka karo na 32. An fara gasar ce tun a…

A yau Juma’a ce ake sa ran za a fara fafatawa a gasar cin Kofin Afirka karo na 32. An fara gasar ce tun a 1957 kimanin shekara 52 da suka wuce.  Tun daga wancan lokaci ake gudanar da gasar duk bayan shekara biyu.

A bana za a gudanar da gasar ce a kasar Masar bayan Hukumar CAF ta kwace ta daga kasar Kamaru ganin ba ta shirya ba.

Da farko kasashe 12 ne suka fafatawa a tsakaninsu daga baya aka mayar zuwa kasashe 16 amma daga bana  Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta kara yawan kasashen da za su fafata daga 16 zuwa 24.

Gasar za ta gudana ce a tsakanin ranakun 21 ga Yuni zuwa 19 ga Yulin bana.

Kamar yadda tarihin gasar ya nuna, mai masaukin baki Masar ce ta fi yawan lashe wannan gasa.  Ta lashe gasar har sau 7 wato a 1957 da 1959 da 1986 da 1998 da shekarar 2006 da 2008 da kuma 2010.

Sai Kamaru wacce ta dauka har sau biyar wato a 1984 da 1988 da 2000 da 2002 da kuma 2017. Sai Ghana da ta dauka sau hudu a 1963 da 1965 da 1978 da kuma 1982.  Sai Najeriya da ta dauka sau uku a 1980 da 1994 da kuma 2013.

Shahararrun ’yan kwallon Afirka da ke wasa a sassan duniya za su wakilci kasashensu irin su Mohammed Salah dan kwallon Liberpool da ke Ingila wanda zai wakilci kasar haihuwarsa Masar sai Sadio Mane dan kwallon Liberpool zai wakilci Senegal da sauransu.  Haka ’yan kwallon Najeriya irin su Wilfred Ndidi da ke wasa a kulob din Leicester City na Ingila zai wakilci Najeriya da sauransu.

Kasar da ta lashe gasar za ta samu kyautar Dala miliyan daya da rabi kimanin Naira miliyan 541 da dubu 500.