Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yau za a fara Gasar Firimiya a Ingila

A yau Juma’a ce ake sa ran za a fara gasar Firimiya ta Ingila. Wannan na nuna yau kakar wasa ta bana take farawa a Ingila inda kungiyoyi 20 za su fafata a tsakaninsu don a samu zakara.

Gasar wacce ke gudana a duk shekara, a bara kulob din Manchester City ne ya lashe.  Kulob din ya lashe ta ce sau biyu a jere inda masana harkar kwallo suke ganin watakila kulob din ya sake lashe ta bana ganin yadda yake da zaratan ’yan kwallo.

ADVERTISEMENT

Kulob din Liberpool da na Norwich City ne za su bude gasar a yau da misalin karfe 8 na dare agogon Najeriya a filin wasa na Anfield, wato gidan Liberpool.

Kamar yadda jadawalin gasar ya nuna, a gobe Asabar za a gudanar da wasanni 6 yayin da a jibi Lahadi kuma za a yi wasanni uku wanda hakan zai sa a yi wasanni 10 a tsakanin yau Juma’a zuwa jibi Lahadi.

ADVERTISEMENT

Ana sa ran gidajen kallon kwallon kafa za cika don ganin yadda wasannin za su kasance.