Search
Subscribe
Yaushe za a daina yayin Ronaldo da Messi?

Yaushe za a daina yayin Ronaldo da Messi?

Yaushe za a daina yayin Ronaldo da Messi?

A daidai lokacin da aka fara shirye-shiryen bayar da Kyautar Gwarzon Dan Kwallon Duniya ta Ballon d’Or, mutane da yawa sun fara hasashen cewa a tsakanin Ronaldo da Messi wani zai lashe kyautar, duk da cewa akwai dan wasan Liberpool Birgil ban Dijk da ya kunno kai.

Kullum duniyar kwallon kafa cike take da muhawara a kan tsakanin Ronaldo da Messi wa ya fi wani. Amma ba ko tantama a kan su biyun suna gaba da kowa, domin an kasa samun wanda zai dusashe tauraronsu har ma ta kai ana tunanin ba a taba samun ’yan wasa ba kamar su a tarihin tamaula.

Abin mamaki shi ne yadda Luka Modric ya yi karkon kifi, inda duk da cewa shi ne mai rike da kambun, bana ba ya cikin mutum 10 da aka fitar.

A baya, an yi zaratan ’yan wasa, tun lokacin su Johan Cruyff da Michael Platini da su Pele da Mardona da sauran takwarorinsu. Har zuwa lokacin su Zinedine Zidane da su Ronaldo na Brazil da Figo da Ribaldo da suransu. Amma a tarihin kwallo ba a taba samun wadanda suka dade suna zamani ba kamar Ronaldo da Messi musamman a shekara goma da suka gabata domin da wuya ka ga dan kwallo ya yi shekara 10 tauraronsa bai dusashe ba ko kuma akalla ya rage haske, amma su abin kara gaba yake yi.

A cikin shekara 12 da suka gabata, sun raba kyautar gwarzon dan kwallo guda 10 na Ballon d’Or a tsakaninsu da ta FIFA guda hudu, sun zura kwallo sama da 1000, sannan da wuya idan akwai wani tarihi da ya rage da ba su karya ba. Tashensu da gasar da ke tsakaninsu sun taimaka wajen gyara kwallo da karin masoya ga wasan. Sannan har yanzu likafarsu kara sama take yi, suna kara shekaru, suna kara kwarewa.

 

Wane ne Ronaldo?

Cristiano Ronaldo dos Santos Abeiro wanda aka fi sani da Cr7 an haifi shi ne a ranar 5 ga Fabrairun 1985 a Tsibirin Madeira da ke kasar Portugal. Shi ne Kyaftin din Portugal kuma yanzu haka yana tare da Jubentus ta Italiya.

Ya fara taka leda ce a Kungiyar Sporting CP da ke Portugal duk da cewa kafin nan ya samu tsaiko lokacin yana dan shekara 15, inda ya yi fama da matsalar cutar bugun zuciya. A shekarar 2003 sai ya koma Manchester United yana dan shekara 18, inda ya lashe Kofin Kalubale (FA) a shekarar farko. Sannan ya lashe Kofin Zakarun Turai daya da Firimiya ta Ingila sau 3 da sauransu.

A shekarar 2009 ya koma Real Madrid, inda ya lashe kofi 15, ciki har da Laliga 2, Copa del Rey 2 da Kofin Zakarun Turai hudu,  sannan ya zama Gwarzon Dan Kwallon Duniya sau hudu a kolub din, inda ya zama yana da jimilla guda biyar da guda daya da ya lashe a Manchester United.

Sannan a kakar bara ya koma Jubentus, inda ya lashe Kofin Seria A da Supercoppa Italiana, sannan ya lashe kyautar dan wasan da ya fi taka leda. Sannan shi ya jagoranci kasar Portugal wajen lashe Kofin Nahiyar Turai da sauransu.

 

Wane ne Messi?

Lionel Andres Messi an haife shi ne a ranar 24 ga Yunin 1987 a Ajentina. Yanzu haka shi ne Kyaftin na Ajentina da Barcelona.

Shi ma lokacin da zai fara taka leda, sai ya samu tsaiko inda ya yi fama da ciwon doro (growth hormone deficiency), wanda ke kawo matsalar rashin girman jiki. Yana dan shekara 13 sai ya dawo kasar Spain, inda kungiyar Barcelona ta dauki nauyin jinyarsa. Daga bisani ya samu lafiya sannan ya fara buga wa Barcelona yana da shekara 17.

Ya lashe kofi 34 da suka hada da Laliga 10, Kofin Zakarun Turai hudu, Copa del Rey 6 da sauransu.

Ya taba lashe Kofin Duniya na ’yan kasa da shekara 20 da gasar Olympic da kasar Ajentina.

 

Yadda suka mamaye kyautar Gwarzon Dan Kwallon Duniya

A shekarar 2007 ce dan wasan Brazil Ricardo Kaka ya lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Duniya, Messi ya zo na biyu, Ronaldo na uku. Tun wancan shekara ba a sake samun wanda ya lashe kyautar ba bayan Ronaldo da Messi sai bara da Luka Modric ya samu. Kuma bana ungulu na neman komawa gidanta na tsamiya.

Ke nan sai da suka dauki kyautar sau 10 a jere a tsakaninsu kafin wani ya samu. Sannan duk a wadannan shekaru, sun zura kwallaye da yawa, sun ci kofuna da dama, sannan sun karya tarihi da yawa.

 

’Yan wasan da Ronaldo da Messi suka hana tashe

Daga cikin wadanda yayi da tashen Ronaldo da Messi ya danne su, inda har suka kasa lashe kyautar gwarzon dan wasa duk da cewa sun kware akwai Dabi da Iniesta da Suarez da Torres da Buffon da Riberry da sauransu. Shi kansa Kaka, ba don Ronaldo da Messi da ya lashe sama da daya.

Akwai kuma irin su Neymar da Griezman da watakila nan gaba za su iya lashe kyautar amma yawanci ana ganin ba a cika zancensu ba, saboda kasancewar Ronaldo da Messi suna nan.

 

Dalilan da ya sa suka dade suna lokaci

Akwai abubuwa da yawa da suka sa suka dade suna jan zarensu, daga cikinsu akwai:

  1. Gasa a tsakaninsu: Kasancewar dukkansu suna da kwazo, hakan ya sa kowane daya ba ya so dayan ya fi shi. Za a ga hakan idan aka lura da yadda Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or hudu a jere, amma hakan bai hana Ronaldo dagewa ya kamo shi ba.
  2. Yawan mabiya: Kasancewar yanzu a kwallon kafa duk an fi kiran sunansu, hakan ya sa suna samun talla da kamfanoni da yawa. Kasancewar suna da alaka da kamfanoni kuma suna da yawan mabiya ya taimaka wajen kara kwazonsu ko ba don kamai ba, domin su biya kamfanoni kudaden da suke biyansu da kuma birge dimbin masoyansu da sauransu.

 

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin