✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yawan fararen hula da ake kashewa a Afghanistan ya karu’

Tashe-tashen hankula a kasar Afghanistan sun yi farar hula kimanin kashi 23 cikin 100 kisan gilla, kamar yadda rahoton Majalisar dinkin duniya ya bayyana.Rahoton, wanda…

 Shugaba Hamid Karzai na AfghanistanTashe-tashen hankula a kasar Afghanistan sun yi farar hula kimanin kashi 23 cikin 100 kisan gilla, kamar yadda rahoton Majalisar dinkin duniya ya bayyana.
Rahoton, wanda daraktan Kula da Hakkin dan Adam na Majalisar dinkin Duniya a Afghanistan ya gabatar, ya bayyana cewa mata da kananan yara su suka fi shan wahala, a wannan yaki da aka shafe shekara 12 ana fafatawa, inda ya bayyana adadin yaran da ya kai kashi 30 cikin 100 na wadanda aka kashe. Yawan farar hular da aka kashe ya kai mutum dubu da 300, sannan akwai mutum dubu biyu 533.
Ganin yadda ake ta yi wa al’umma kisan kiyashi, ta sanya masana ke hasashen da wuya kasar Afghanistan ta iya shawo kan ’yan Taliban, da zarar sojojin kasashen waje sun janye daga kasar.