✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawan rikice-rikice: Tsakanin gwamnati da sarakuna da jami’an tsaro wa ya fi sakaci?

A daidai wannan lokaci da kasar nan ke fama da rikice-rikice, yawanci ana kai-komo wajen nuna yatsa da zargi a kan tushen rikici amma kusan…

A daidai wannan lokaci da kasar nan ke fama da rikice-rikice, yawanci ana kai-komo wajen nuna yatsa da zargi a kan tushen rikici amma kusan kowa ya yarda cewa akwai sakaci daga wani bangare. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan wai tsakanin gwamnati da sarakuna da jami’an tsaro, wane bangare ne ya fi sakaci? Ga abin da mutane suke fada:

 

Gwamnati ta fi sakaci – Nafisa Mustapha

Daga Jamilu Adamu

Nafisa Mustapha Sabon gari Zariya: “Gwamnati ce mai sakaci a kan rikice-rikicen wannan kasar. Dalili kuwa shi ne idan ka duba jami’an tsaro da muke da su a kasar nan sun yi kadan kuma da kyar gwamnati ke ba su albashinsu kuma albashin na su baya isarsu. Dalilina na biyu shi ne rashin aikin yi a kasa yana jawo rikice-rikice, kuma hakki ne na gwamnati ta samar wa ‘yan kasa aikin yi. Sau da yawa gwamnati za ta kama masu laifi amma a kasa hukuntasu wannanma yana jawo rikice-rikice a kasa.

Daga karshe ina baiwa gwamnati shawara da ta samar da jami’an tsaro isassu a kasa, sannan ta kula sosai da hakkokinsu, kuma a kula wajen hukunta masu laifi.”

 

Gwamnati ke da laifi dari bisa dari – Ahmad Badamasi

Daga Jamilu Adamu

Ahmad Badamasi Tudun Jukun Zariya: “Gwamnati ke da laifi dari bisa dari. Wannan rikice-rikicen na faruwa ne sakamakon rashin aikin yi da matasa suke fama da shi, wasu jihohin ma korar ma’aikatanta take yi sakamakon rashin aikin yi dole matasa su samawa kawunansu aikin yi ta hanyar ba su wani abu kalilan domin su tada hankulan jama’a. Sannan gwamnati ta sama wa jami’an tsaro isassun kayan aiki domin jami’an tsaron suna kukan rashin isassun kayan aiki na zamani. Ina rokon Allah da Ya ba mu zaman lafiya a jiharmu da kasa baki daya.”

 

Laifin na gwamnati ne – Fatima Bintu Abubakar

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Fatima Bintu Abubakar:  A nata ra’ayin game da wannan batu ta nuna ba laifin kowa ba ne illa na gwamnati, don gwamnati ita ce uwa-ma-ba-da mama don sai ta bari abubuwa suke lalacewa.  Ta ce idan aka dubi yadda gwamnati ke yi wa harkar tsaro rikon sakainar kashi, da hakan ke jefa al’umma cikin matsala, wannan ya nuna ita ya kamata a dora wa wannan laifi.  Alal misali, idan wani hargitsi ya tashi kuma aka yi nasarar kama wadanda suka tayar da shi, sai ka tarar babu wani kwakkwaran hukunci da ake yanke musu, hasalima a wasu lokutan a kan saki irin wadannan bata-gari ne, to ta yaya irin wadannan mutane ba za su sake tayar da wata fitinar ba don sun san ko sun tayar babu abin da za a yi musu.

 

. Sarakuna sun fi laifi – Abdullahi Hussaini

John Wada, Nasarawa

Abdullahi Husseini: “Ba shakka sarakuna ne suka fi laifi. Saboda ka san su ne suka fi kusa da jama’a. Ma’ana su suka fi sanin mutanensu. Inda suna tsawata musu suna jan kunnensu a kowane lokaci da an dade da magance matsalar. Gwamnati da jami’an tsaro ba su san wadannan mutanen kamar yadda sarakunan suka sansu ba. Saboda haka a takaice zan dora laifin a kan sarakuna ne.”

 

Na fi dora laifin ga gwamnati – Akulo Yohana

Akulo Yohana: “Ni dai a kullum ina dora laifin ga gwamnati ne. Dalili kuwa shi ne ka ga da jami’an tsaron da sarakunan duk kamar yadda ka sani suna karkashin gwamnati ne. Gwamnati tana da iko ta tura su su magance rigingimun ko a ina ne. Haka kuma sau da yawa idan aka yi rikici tsakanin mutane aka kai su kotu, za ka tarar wanda aka kama shi da laifi maimakon gwamnati ta hukuntashi don ya kasance darasi ga saura, sai su ki yin haka.  Shi ya sa nake dora laifin ga gwamnati.”

 

Gaskiya laifin na kowa ne – Ummulsalma Ibrahim

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Ummulsalma Ibrahim:  “Gaskiya ina ganin laifin na kowa ne ma’ana na gwamnati ne, na sarakuna ne, sannan na jami’an tsaro ne.  Dalilin fadin haka kuwa shi ne akwai lokacin da za ka tarar gwamnati ta yi kokarin kawo karshen matsalar tsaro amma bangaren jami’an tsaro sai su yi wa abin kutungwila ta hanyar hada kai da batagari ana aikata ba daidai ba.  Sannan an sha samun labarin yadda wadansu sarakunan gargajiya suke hada kai da batagari ana aikata ba daidai ba a cikin al’umma.  Yayin da ita kuma gwamnati a wani lokaci takan yi sakaci har sai abu ya kazance kafin ta dauki matakin magance shi.  Don haka matsalar yawan tashin rikici a kasar nan za a iya dora shi a bangaren gwamnati da na sarakuna da kuma na jami’an tsaro.