✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Ya’ya sun yi garkuwa da mahaifinsu mai shekara 88

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta gabatar da wadansu matasa biyu mace da namiji masu suna Chinaza Nwogu da  Emeka Ejike kan zarginsu da laifin hada…

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta gabatar da wadansu matasa biyu mace da namiji masu suna Chinaza Nwogu da  Emeka Ejike kan zarginsu da laifin hada baki da wani mai suna Emmanuel Sunday don yin garkuwa da mahaifinsu Louis Njoku mai shekara 88.

Kakakin Rundunar  ’Yan sandan Najeriya, Frank Mba wanda ya gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai, ya ce kama matasan na da nasaba da wadanda ake zargi da kashe wani da ya kammala yi wa kasa hidima. Kuma wannan nasarar na cikin aikin Operation Puff Adder da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya kaddamar.

Frank Mba, ya ce “Ina hedkwatar Rundunar ’Yan sandan Jihar Imo tare da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya. Sannan an gabatar da Chukwuemeka Eze, wanda ya kashe watada ta kammala yi wa kasa hidima (NYSC) mai suna Lillian Mgbanwu bayan ya yi mata fyade.”

A ranar 7 ga Yuli, aka kama Chukwuemeka Eze, ya dauki wata wayar salula a wani shagon Ahamefule Onyeka, amma ya ki amincewa da laifinsa ya nuna cewa, ya kai cajin wayar ce zuwa shagon. Ahamefule, ya kai kara kan daukar wayar ga ofishin ’yan sandan da ke Oru ta Yamma. Bayan binciken ’yan sandan sun tabbatar da cewa, ya dauke wayar wadda ta kammala yi wa kasa hidimar ce tare da yi mata fyade sannan daga bisani ya kashe ta.

Rundunar ’Yan sandan ta ce, wannan ba karamin laifi ba ne, kuma ta yi alkawarin tabbatar da adalci wajen gudanar da binciken.

Matasan biyu namiji da mace da suka kintsa garkuwa da mahaifinsu mai shekara 88, an gano Emeka Ejike mijin ’yar wanda aka so yin garkuwa da shi ne.

“Chinaza ta auri Emmanuel, kuma ta hada baki da dan uwanta don yin garkuwa da mahaifinsu, wannan shirin yin garkuwan na da alaka da hadin bakin mata da miji da dan uwa,” inji ’yan sandan.

A cewar Frank Mba ya fahimci cewa, Emmanuel ya yi shirin ya yi amfani da kudin fansa na Louis Njoku, don ya biya sadakin aurensa.

Frank, ya kara da cewa, ’yan sanda masu yaki da garkuwa da mutane ne suka kama wadanda ake zargin a ranar 29 ga Yunin bana tare da samunsu da laifuffukan aikata yin garkuwa da mutane.

Wadanda aka kama sun shahara wajen yin garkuwa da mutane a garin Mbaise da kewayenta don karbar kudin fansa, sun kuma amsa laifin da ake tuhumar su da shi a gaban ’yan sanda, yayin da suka bayyana yadda suke gudanar da ayyukan garkuwa da mutane a garuruwan yankin.