✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Ya’yan PDP 500 sun canja sheka zuwa APC a Jihar Kogi

Rahotanni sun ce akalla mambobin Jam’iyyar PDP 500 ne suka sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Lakwaja da ke Jihar Kogi. Masu sauya…

Rahotanni sun ce akalla mambobin Jam’iyyar PDP 500 ne suka sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Lakwaja da ke Jihar Kogi. Masu sauya shekar, sun ce sun yanke shawarar ce domin nuna biyayyarsu ga Gwamna Yahaya Bello, inda suka samu tarba daga Malam Muhammed Dan’asabe Muhammed, wanda ya wakilci Gwamnan a wurin taron karbar nasu. A jawabinsa ya ce masu sauya shekar sun yanke shawara mai kyau ta hanyar dawowa ga jam’iyyar ci gaba.

Ya ba su tabbacin cewa jam’iyyar za ta tabbatar da adalci da daidaito ga dukkan ’ya’yanta a koyaushe, ba tare da la’akari da lokacin da suka shigo jam’iyyyar ba. Muhammed ya bukaci ’ya’yan jam’iyyar su ci gaba da kintsa kansu da kuma aiwatar da abubuwan da za su kare martabar jam’iyyar. Ya yi kira ga wadanda suka sauya shekar su tabbatar an sake samu karin mutane da za su sauya sheka zuwa jam’iyyar, inda ya ce gwamnatin jihar ba za ta hana adawa ba domin siyasa ta fi dadi idan akwai abokan hamayya.

A jawabin shugaban masu sauya shekar, Alhassan Gimba, ya ce sun koma APC ne domin ganin dimbin nasaraorin da Gwamna Bello ya samu a zangon mulkinsa na farko.