Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yayin da aka cire takunkumin yakin neman zabe

A ranar lahadi 18 ga wannan watan ne aka dage takunkumin yakin neman zabe wanda ya bayar da dama ga ‘yan siyasan kasar nan su fara kamfen domin neman mukamai daban-daban a kasar nan.

A dalilin haka ne ya sanya shugabanni ke ta yin kiraye-kiraye domin ganin an gudanar da kamfen din cikin kwanciyar hankali tare da nuna halin dattako da sanin ya kamata.

ADVERTISEMENT

Shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya a ranar Lahadi ya bukaci ‘yan siyasa su kula kada su kunna wa kasar nan wutar fitina a yayin gudanar da yakin neman zaben da suke yi.

Haka shi ma Mai martaba Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya shawarci ‘yan siyasa su gudanar da harkokinsu ba tare da hatsaniya ba. Haka dai shugabanni na siyasa da na addini suke ta kira ga ‘yan siyasa domin su gudanar da yakin neman zaben cikin lumana da kwanciyar hankali.

ADVERTISEMENT

Lallai kam yanzu an shiga wani lokaci da ya kamata a kula sosai domin kada a tayar da fitinar da za ta zama matsala ga kasar nan har ta kai ga an kasa gudanar da zaben ma gaba daya. Domin a yayin yakin neman zabe ‘yan siyasa suna amfani da munanan kalamai da amfani da ‘yan banga da suke tayar da hankali a sanadiyyar haka har a kai ga rasa rayuka da barnata dukiya.

Saboda haka akwai bukatar matasa su kula, kada su yarda ‘yan siyasa su yi amfani da su wajen tayar da hankali domin cim ma burinsu na siyasa, domin da zarar bukatarsu ta biya za su yi watsi da su ne, ba za su sake nemansu ba sai wani zaben ya taso. Za su ingiza su su kashe kawunansu ko su nakasa kawunansu alhali su ‘ya’yansu suna kwance a gidajensu, ku kuwa sun jawo wa iyayenku asara.

Duk dan siyasan da ya zo yakin neman zabe mutane su tsare shi ya yi masu bayanin abin da ya yi masu, idan wanda aka zaba a baya ne ya dawo yana neman a sake zabensa, idan kuma sabo ne sai a zaunar da shi a bukaci ya bayyana irin ayyukan alherin da ya yi wa jama’a tanadi, su kuma masu zabe su bayyana masa abubuwan da suke bukata, maimakon. su bari dan siyasa ya ba su dan abun da ba zai kashe masu kishi ba, shi yake sanyawa idan ya ci zabe yake ganin kudinsa ne ya ba shi, domin haka sai ya yi watsi da bukatun jama’a ya mayar da hankali wajen mayar da kudinsa tare da cin riba.

Yanzu ba siyasar akida ake yi ba, siyasa ce ta neman mukami ko ta wane hali, shi ya sanya ake ganin ‘yan siyasa suna canja sheka babu kakkautawa, yau suna wannan jam’iyya, gobe suna wancan, domin samun biyan bukatarsu ta darewa wata kujera da suke hari. Saboda haka kada wani ya tayar da hankalinsa saboda da wani zan takara, domin mafi yawansu ba talakawa ne a gabansu ba, sun zuba jari ne suna nema yadda za su ci riba. Domin haka a rika kula da cancanta ba jam’iyya ba, yanzu babu maganar guguwa ko sak, domin a baya an yi guguwa mun ga irin kwashi-kwaraf din da ta jawo mana, saboda haka bai kamata a sake maimata kuskuren ba, duk inda mutumin kirki yake ko a wace jam’iyya yake shi za a zaba, a tara mutanen kirki daga jam’yyu daban-daban ya fi a kwaso shirmanmu daga jam’iyya guda, domin daga baya za su watse su koma wadansu jam’iyyun idan ba su samu abin da suke nema ba.

Yanzu mulkinn demokaradiyyar kasar nan ta shekara kusan ashirin, lokaci ya yi da mutane za su daina barin ‘yan siyasa suna wasa da hankulansu, lallai ne su jajirce su rika zaben masu kishinsu ba masu kishin aljihunansu ba.

Mutanen kudancin kasar nan ba su zaben kowane irin mutum sai sun tabbatar zai kare muradunsu, amma a yankin Arewa duk wanda yake da kumbar susa ko ya shiga inuwar wani dan takara sai a zabe shi ba tare da an tabbatar zai iya daukar amanar da aka dora masa ba. Shi ya sanya yankin Arewa yake samun matsala, musamman a majalisa, saboda wakilan yankin da damansu ba su san abin da ya kai majalisar ba, sun tafi ne kawai su dumama kujera, wadansu ma sai su dade ba su je majalisar ba balle a ji duriyarsu.

Wajibi ne a rika la’akari da ilimi da gogewar dan takara kafin a zabe shi, domin ta haka ne za a rika samun biyan bukatar zaben da aka yi.

A janhoriya ta biyu da yake a lokacin ba a sanya batun matsayin ilimi a cikin sharuddan tsayawa takara ba, an zabi ‘yan majalisun da suka zama abin dariya domin ba su san abin da ake yi a majalisa ba,  sai dai su zauna ko su ruka barci, idan za a yi kuri’a a kan wani muhimmin batu idan akwai wani a kusa da su sai ya tashe su ya ce su daga hannu, sai su daga hannunsu alhali ba su san a kan mene ne suka daga gannun ba.

To yanzu an sanya matsayin ilimi a cikin sharuddan tsayawa takara, domin haka lallai ne a rika zaben wadanda za su iya gwagwagwa da takwarorinsu na kudancin kasar nan a majalisar kasa, kada a tura wadanda za su sayar da mutuncin yankinsu saboda jahilci. Domin kuwa kalmar guda daya kawai za a yi amfani da ita a kifar da su ba su sani ba saboda rashin sanin lugga.

Abin da ya faru a baya lokacin mulkin shugaba Obasanjo da ‘yan majalisar yankin Arewa suka amince a rika ba jihohin da ake samun man fetur a cikinsu kaso daga kudin man da ake samu a kan tudu da kuma na ruwa, alhali na kan tudu kawai ake ba su, ya isa misali. Domin rashin zurfin ilimi ne ya jawo haka, shi ya sanya yanzu wata jiha a yankin da ke samar da mai take samun kudin da ya kusan na jihohin Arewa gaba daya, su kuma jihohin Arewa an barta da lalita mara nauyi.

Saboda haka lokaci ya yi da mutanen yankin Arewa za su farka su rika zaben mutanen da suka cancanta ba bara-gurbi ba wadanda za su kai yankin su baro.