✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yayin da gobe take zabe

Gobe Asabar, 16 ga Fabararu, 2019, insha Allah,  ’yan Najeriya za su fita domin su kada kuri’unsu. Koda yake sama da mutum miliyan 80 suka…

Gobe Asabar, 16 ga Fabararu, 2019, insha Allah,  ’yan Najeriya za su fita domin su kada kuri’unsu. Koda yake sama da mutum miliyan 80 suka yanki katin zabe, amma yana da wahala kowa ya fita ya yi zabe. Gobe za a yi zaben Shugaban kasa da na ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa (Dattawa da Wakilai). Sannan ranar 2 ga watan Maris mai zuwa a gudanar da na gwamnonin jihohi da na ’yan majalisar jihohi.

Babbar damuwar ’yan Najeriya ita ce a yi zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da an kashe ko kiyashi ba. Wannan bai yiwuwa sai an tabbatar da wasu abubuwa kamar haka: Na farko a kiyaye ’yancin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta  ta Kasa (INEC), ta gudanar da zaben ba tare da manakisa ko tankwasa ta ba. Dole ne hukumar zabe ta nuna da gaske ita mai cin gashin kanta ce. Ya kamata hukumar ta guji yin duk wasu abubuwa da za a zarge ta cewa tana nuna goyon bayan wani dan takara ko wata jam’iyya.

’Yan sanda: Idan Najeriya na so ta inganta mulkin dimokaradiyya ba kama-karya, dole a yi wa aikin dan sanda garambawul ya dace da tsarin dimokaradiyya. Gaskiya, tsohon Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya raunana mutuncin aikin, saboda takaddama da ya samu cikin wasu badakaloli da ake ganin ya sanya siyasa a ciki. Irin wannan ke zubar da mutuncin aikin, ya sa wadansu mutane ke kallon ’yan sanda sun zama karnukan farautar masu mulki. Mu dai mun san muhimmancin aikin dan sanda, kuma kundin tsarin mulkin Najeriya, ya bayyana komai game da aikin dan sanda. Dan sanda kasa yake yi wa aiki ba wadansu mutane ba, amma a Najeriya inda aka fi fifita masu rike da madafun iko, na nuna dan sanda an yi shi ne kawai domin ya kare manya. To a gaskiya in har ’yan sanda suka gaza tashi tsaye lokacin zaben nan, to wadansu ’yan iska za su yi amfani da wannan dama su yi kokarin tada rikici lokacin zabe ko bayan an kammala zabe. Abin da ya faru a wasu kananan hukumomin Jihar Katsina da suka hada da Charanchi, Bindawa, Jibiya, Kaita, Safana da Batsari, inda ’yan bangar siyasa suka yi bore cewa, wai dole sai an dauki ’yan asalin kananan hukumomin aikin wucin gadi na zaben, kuma wadannan ’yan bangar siyasa sun yi abin nan a gaban ’yan sanda, na nuna cewa babu wani tabbas ko ’yan sanda za su iya samar da wani tsaro lokacin zaben. Mun fa gani a gaban ’yan sanda ake tozarta ma’aikatan wucin gadi na hukumar zabe, kuma babu wani mataki da suka dauka. An samu wannan rikici tun a lokacin horar da ma’aikatan wucin gadin, to ina ga a zo ranar zabe? Muna ganin kodai hadin baki ne a tsakanin wadansu ’yan siyasa da jami’an tsaro, ko jami’an tsaron ne ba su san aiki ba.

Kalaman tozartawa da tunzurawa daga bakin manyan ’yan siyasa da shugabanni na cikin abubuwan da in ba a yi hattara ba, za su kawo rikicin zabe. Misali, kalaman Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, inda ya yi barazanar cewa duk ’yan kasashen waje da suka kuskura suka yi katsalanda a cikin zabe, za a mayar da gawarwakinsu gida. Wannan kalaman mai ilimi ne, to ina ga dan bangar siyasa wanda ko makarantar kirki bai je ba?

Kuma abin mamaki irin wadannan kalamai ne fadar Shugaban Kasa ta fito tana karewa inda muka ji Garba Shehu, Kakakin Fadar yana cewa, kishin kasa ne, ya sa El-Rufa’i ya furta wadannan kalamai. To idan gwamnati, wadda ke ikirarin kawo canji ke goyon bayan kalaman kiyayya, wa zai iya dakile rikicin zabe?

Mun ga yadda gwamnoni suka gudanar da yakin neman zabensu. Mun ga irin yadda ake yawo da ’yan bangar siyasa dauke da miyagun makamai, suna ihu suna kirari cewa dole jam’iyyarsu sai ta yi. Kuma kowa ya san cewa da ’yan bangar siyasa ake amfani a tada zaune-tsaye. Wani dan sanda ya ce a gabansu a gidan gwamnatin wata makwabciyar Jihar Katsina, ake raba wa ’yan banga kwaya da Naira dubu uku kafin a tafi yakin neman zabe. Don haka mutanen da ake gani dauke da takubba da barandami a ayarin kamfen, dauko su haya aka yi ana biyansu, kuma suna da goyon bayan wadansu manyan mutane.

Irin abin da ke faruwa a wannan zaben, ga alamu babu wani darasi da ’yan siyasar Najeriya suka koya. Babu wani darasi da matasan Najeriya suka koya. Kowa jam’iyyarsa ba ta laifi, sai wata jam’iyyar. Wannan ba daidai ba ne. Kasar nan, mun san inda aka taho, mun san rikice-rikicen zabubbukan da aka yi suka koma na addini, mun kuma san yawan wadanda aka kashe, akasari, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. Don haka ya kamata mu yi hattara, nawa ake biyan mutum a siyasar? Siyasar ma da ake ta yaudara, ka ga barawo an kama shi kace-kace yana karbar cin hanci, amma don rashin tsoron Allah mun yi kememe muna kare shi.

Mu daina bari saboda yunwa da talauci, mu sayar da tunaninmu da ’yancinmu na fadin albarkacin baki. Wani sakaren kan Naira dubu uku, sai ya tado da bala’in da za a rasa rai.

Duk kalaman batanci da na kiyayya na ji da karantawa za ka samu ’ya’yan marasa shi ne, wadanda, wadatar kirki ma ba ta ishe su ba, ana ba su dan abin da bai taka kara ya karya ba, suna yada kalaman kiyayya da cin mutuncin manyan mutane ba tare da la’akari da al’adunmu da addininmu ba.

Kowa ya yi nazari, kasar nan, kashi nawa cikin dari ke iya samun ingantaccen ilimi daga matakin firamare zuwa jami’a? Mutum nawa idan matansu za su haihu, ba sa shiga halin kunci saboda ba su da kudaden da za su biya a asibiti? Mutum nawa ya fi karfin abinci sau uku kullum? Mutum nawa ke da muhalli na kansa? Mutum nawa ke da cikakkiyar sana’a da ke iya rike shi ba tare da buge-buge ba? Wadannan su ne ya kamata su yi mana jagora gobe in mun zo kada kuri’unmu ba sakarci da siyasar son rai ba.

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina Babban Sakataren Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa ,08165270879.