✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yobe: RATTAWU ta fara yajin aiki don rashin biyan ’yan kungiyar hakkokinsu

kungiyar Ma’aikatan Gidajen Rediyo da Talabijin da Wasan Kwaikwayo ta kasa reshen Jihar Yobe (RATTAWU) za ta fara da yajin aiki sai baba-ta-gani har sai…

kungiyar Ma’aikatan Gidajen Rediyo da Talabijin da Wasan Kwaikwayo ta kasa reshen Jihar Yobe (RATTAWU) za ta fara da yajin aiki sai baba-ta-gani har sai gwamnatin jihar ta biya musu bukatunsu.
Bayanin hakan dai fito ne a cikin takardar sanarwar mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya ta Jihar Yobe Kwamred Yusuf Isa da kuma Shugaban kungiyar RATTAWU na jihar Kwamred Saleh Musa Gulani  bayan dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki uku da uwar kungiyar ta kasa ta ba da sanarwa ga ’ya’yanta.
Takardar ta ce babban abin da ya dami kungiyarsu shi ne yadda gwamnatin jihar ke jan kafa wajen biyansu hakkokinsu, duk da takardun da suka rika rubutawa, amma shiru babu kwakkwarar magana game da batun.
Sanarwar ta ce babbar bukatarsu ita ce, neman a biya su alawus-alawus dinsu a matsayinsu na ma’aikatan gidajen rediyo da talabijin da sauran bukatu kamar yadda aka tsara a matakin kasa, musamman ganin cewar tuni takwarorinsu na wadansu jahohin suka fara cin gajiyar karin.
Don haka ne suka yanke shawarar ci gaba da wannan yajin aiki na sai da nufin sai an biya musu bukatunsu kamar sauran ’yan uwansu da ke wadansu jahohin kasar nan.
Sanarwar ta bukaci dukkan ’yan kungiyar su ci gaba da nuna juriya tare da bada hadin kai har sai an  kai ga nasarar samun biyan bukatunsu.
Sanarwar ta umarci ’yan kungiyar su dakatar da aikin wucin gadi da aka rika yi a baya har sai an kai ga cimma buri, kuma koda wane tsawon lokaci za a dauka.