✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yobe ta kashe Naira biliyan 1.8 don inganta ilimi

Gwamnatin Jihar Yobe ta ce ta kashe Naira biliyan daya da miliyan 790 daga shekarar 2011 zwa 2015 a fannin ilimi a kokarin da take…

Gwamnatin Jihar Yobe ta ce ta kashe Naira biliyan daya da miliyan 790 daga shekarar 2011 zwa 2015 a fannin ilimi a kokarin da take yi don habaka ilimi a matakin farko na firamare da karamar sakandare.
Babban Sakataren Hukumar Bayar da Ilimi Bai-daya na Jihar Yobe (SUBEB), Alhaji Goni Ibrahim ya bayyana haka lokacin da Babban Sakataren Hukumar UBE ta kasa Alhaji Dikko Suleiman ya kai ziyara jihar don duba harkokin hukumar musamman manyan matsalolin da take fuskanta sakamakon rikicin Boko Haram.
Sakataren ya ce, gwamnatin jihar ta kafa kwamiti na musamman da ke bin diddigin duk ayyukan da aka gudanar a hukumar don tabbatar da komai an gudanar da shi ba cuta ba cutarwa.
Alhaji Goni, ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kebe kusan Naira biliyan 1 da miliyan 200 a bana don ci gaba da gudanar da ayyukan hukumar da suka hada da gina ofisoshin hukumar a wasu wurare tare da sababbin gine-gine a wasu makarantun firamare takwas da kuma gyara makarantu 11 da ’yan Boko Haram suka kona.
Ya ce hukumar za kuma ta sayo littattafan karatu kimanin dubu bakwai sai kuma littattafan koyar da darasin kimiyya da kere-kere guda dubu 30 hade da kujeru da teburan roba 1,150.