✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunkurin juyin mulki a Habasha

A safiyar Asabar 22 ga watan Yunin bana ne mutanen kasar Habasha da sauran mutanen Afirka suka tashi da alhinin wani labari da ke cewa…

A safiyar Asabar 22 ga watan Yunin bana ne mutanen kasar Habasha da sauran mutanen Afirka suka tashi da alhinin wani labari da ke cewa an yi yunkurin juyin mulki a kasar. Wannan yunkuri dai wata alama ce da take nuna yadda tsananin kabilanci da bangaranci ya munana a tsakanin masu rike da madafun iko a waccan kasa. A yayin wannan yunkurin juyin mulki da aka so yi wa Firayi Ministan Habasha, Abiy Ahmed an kai hare-hare har sau biyu, na farko a Bahir Dar, hedkwatar Lardin Amhara da kuma wanda aka kai a Addis Ababa babban birnin kasar. Wadannan hare-hare sun yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama ciki har da na Shugaban Lardin Amhara da kuma Babban Hafsan Sojin kasar da kuma wasu kusoshin gwamnatin kasar da dama.

A sanarwar da ta fitar, gwamnatin kasar ta ce harin da aka kai a Bahir Dar yunkuri ne na juyin mulki wanda wani tsohon Janar na soja mai suna Asamney Tsige ya kitsa. Kuma shi kansa Janar Tsige din ya rasa ransa a ciki a yayin musayar wuta. An ruwaito cewa gwamnatin hadaka ta kasar tana fama da kalubalen rarrabuwar kai na kabilanci. Rahoton ya ci gaba da cewa ‘wannan kisa na 22 ga watan Yuni,  wata manuniya ce ga irin hadarin da ake fuskanta na bai wa wadansu masu tsananin ra’ayin kabilanci jagorancin harkokin tsaro,  domin za su yi amfani da wannan dama wajen ingiza jama’ar kasar Habasha cikin rudani na kabilanci.’

An zargi wadansu mutane sanye da kayan soja da kisan fiye da mutum 50 tare da raunata fiye da 23 wadanda suka hada da mata da yara a yankin Metakal da ke a Lardin Benishangul-Gumuz na kasar. Shugaban Kwamitin Zaman Lafiya na lardin ya ce gwamnatin kasar ta nuna yatsa tare  da zargin Asamnew da ba da horo ga masu tayar da kayar baya da kuma jami’an ’yan sanda da nufin kai hare-hare ga sauran larduna da suke makwabtaka da su, da kuma kalubalantar Gwamnatin Tarayyar Kasar. An dai tsare Asamney a gidan kaso a shekarar 2009 sannan aka sake shi a shekarar 2018 bayan da Firayi Minista Abiy ya yi masa afuwa.

Jim kadan bayan an sako shi, a cikin watan Satumba 2018, wadansu shugabanni a Lardin Amhara sun yi hayar Asamnew a matsayin Shugaban tsaro na lardin. Bayan da ya kama aiki ya yi alkawalin kare ’Yan kabilar Amhara wadanda su ne kashi 28 na jama’ar kasar ta Habasha.  An ga Asamney a wani faifan bidiyo yana yi wa shugabannin addini na wannan yanki jawabi yana fada musu su shirya sadaukar da rayukansu don ’yanto wannan lardi daga kaka gida da aka yi musu.

Gwamnatin kasar ta kama daruruwan mutanen da take zargi suna da hannu a wannan yunkuri na kifar da gwamnati da bai yi nasara ba. Firayi Ministan kasar a makon jiya ya bayyana cewa suna rike da mutum 212 daga Lardin Amhara da ake zargi da hannu a cikin wannan lamari. Da kuma wadansu 43 da aka kama a Addis Ababa.  Christian Tadele, mai magana da yawun jam’iyyar adawa ta National Mobement of Amhara (NAMA) ya zargi gwamnatin kasar da kama ’ya’yan jam’iyyarsu da dama.

Wannan mummunan abu da ya auku a ranar ta 22 ga Yuni yana barazana ga kasar ta Habasha, wanda ya ja hankullan jama’a da dama a wannan kasa mai samun bunkasar tattalin arziki da take da yawan jama’a miliyan 105 bisa alkalumar kidayar shekarar 2017. Haka kuma tana daya daga cikin sannannun kasashe Afirka. Kasar Habasha tana daya daga cikin kasashe masu tasowa da suke samun tagomashin bunkasar tattalin arziki, inda tattalin arzikinta ya habaka da kashi takwas cikin 100, wanda haka ya sanya ta a kan gaba wajen bunkasar tattalin arziki a Nahiyar Afirka baki daya.

Don haka ne ma wannan lamari da ya faru ya saka mu cikin damuwa ganin cewa wannan kasa ta dade tana zaune lami lafiya tun 1991. Kwana kwanan nan ne ita kanta kasar ta Habasha ta shiga gaba wajen sasanta bangarorin da ba sa ga maciji na kasar Sudan. Duk da cewa wannan juyin mulki bai yi nasara ba, amma zai yi wa Firayi Minista Abiy wahalar gaske ya samu kan shugabannin kabilu a zaben da kasar za ta gudanar a badi. Wani mai bai wa Kungiyar Tarayyar Afirka (AU), shawara, Berhutesfa Costantinos ya ce kasar Habasha tana cikin wani hali na kaka-ni-ka-yi.

Shugabannin kasashen Afirka ba zai yiwu su tsoma wa mahukuntan kasar baki ba, tunda yake Habasha kasa ce wadda ta ci gaba fiye da shekara 3,000 da suka gabata. Ba kamar sauran kasashen Afirka ba, kasar Habasha ba ta taba fadawa a karkashin mulkin mallaka ba duk da yake tarihi ya nuna an an taba mamaye ta, kuma an taba samun bore da kuma Yakin Basasa. Amma duk da haka kasar na bukatar ta saita bunkasar tattalin arzikinta da kuma dambarwar siyasar da ta addabe ta. Babban birnin Habasha, Addis Ababa dai shi ne hedkwatar Kungiyar AU, don haka ko ba komai ya kamata mahukuntan wannan kasa su jajirce wajen maido da zama lafiya a kasar domin daga na gaba ake gane zurfin ruwa.