Makarantu za su koma karatu daga ranar 14 ga watan Satumba a Jihar Legas, bayan rufe su sakamakon watan bullar cutar coronavirus tun a watan Fabrairu.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar cewa jihar za ta bude manyan makarantu a ranar 14 ga watan Satumba, kafin makarantun firarmare da sakandare da akwai yiwuwar bude su a ranar 21 ga watan na Satumba.
“Ina farin cikin sanar da cewa za a bar manyan makarantu su bude daga ranar 14 ga Satumba, 2020; Dukkannin manyan makarantu”.
“Game da makarantunmu na firamare da sakandare kuma, muan kokaringanin bude su a ranar 21 ga watan Satumba, 2020.
“Wannan ba kamar wahayi ba ne, za a iya sauyawa gwargwadon abun da Ma’aikatar Lafiya da ke lura da yadda ake bin matakan kariyar cutar ta lura”, inji gwamnan.
Tun a watan Maris gwamnati ta rufe makarantu a fadin Najeriya a kokarin dakile yaduwar cutar coronavirus, wadda ta fara bulla a Jihar Legas a Najeriya.
A ranar 4 ga Agusta aka bude makarantu ga dalibai masu rubuta jarbawar kammala sakandare domin rubuta jarabawar WAEC, wanda aka fara a ranar 17 ga watan na Agusta.