✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a bude makarantun Gwamnatin Tarayya 12 ga Oktoba

Jihohi sun samu izinin bude makarantunsu cikin kiyaye matakan kariyar COVID-19

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin bude makarantun sakanadarenta na hadin kai daga ranar 12 ga Oktoba, 2020.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya ba da umarnin, yana mai cewa an ci karfin cutar COVID-19 da ta tilasta rufe makarantu a Najeriya.

“Mun yanke shawarar bude dukkannin makarantunmu na hasin kai guda 104 daga ranar 12 ga Oktoba, 2020”, inji ministan baya wanta ganawa da Kwamitin Shugaban Kasa na Yaki da COVID-19, a ranar Juma’a.

Ya kuma ba wa jihohi izinin bude makarantunsu cikin cikakkiyar kula da kuma kiyaye matakan kariyar cutar.

Sai dai har yanzu ministan bai sanar da lokacin da za a bude manyan makarantu ba.

A makonnin baya ya sahale wa Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) da ta ba wa jami’o’i izinin fara yin shirye-shirye nan take domin ci gaba da harkonkin karatu.

NUC ta umarci dukkannin shugabannin jami’o’i da su fara shirye-shirye nan take domin ci gaba da karatu baya rufe sakamakon bullar cutar COVID-19.

Umarnnin nata na zuwa ne duba da raguwar masu cutar da bullarta ta sa aka rufe makarantun a ranar 23 ga watan Maris, 2020.

“Sakamakon jawabin Kwamitin Shugaban Kasa kan Yaki da COVID-19 cewa an samu raguwar masu cutar sosai, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta amince da bukatar NUC na cewa jami’o’i su fara shirye-shirye nan take domin ci gaba da harkokin karatu”, inji sanarar.

Sai dai ta gindaya sharudda biyar da suka wajaba kowace jami’a ta cika kafin a bude ta domin gaba da karatu.

  1. Dole a kiyaye matakan kariyar da tsare-tsaren Hukumar Yaki da Cutttuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) na hana yaduwar cutar.
  2. Babu dalilin da zai sa a rusa tsarin zangon karatun NUC da ya danganci adadin kwanakin kowane zangon karatu.
  3. Dole ne a tabbatar da kiyaye dukkannin dokoki da ka’idojin NUC na tabbatar da inganci.
  4. NUC da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya za su kai ziyarar gani da ido domin tantance irin tsare-tsaren kare lafiya da ingancinsu a jami’o’i ta bangaren kayan aiki, dakunan karatu, ofisoshi, ajujuwa, dakunan kwanan dalibai, dakunan gwaje-gwaje, cibiyoyin kula da lafiya da sauransu.
  5. Dole ne daga lokaci zuwa lokaci jami’o’in za su rika sanar da NUC game da halin da suke ciki.