Da Dumi Dumi

Za a daina amfani da nau’ar BAR a Ingila

Rahotanni da ke fitowa daga Ingila sun nuna akwai yiwuwar a daina amfani da na’urar tantance shigar kwallo a raga (BAR) saboda yadda ake yawan samun matsala.

Cece-ku-cen da aka samu a ranar bikin sabuwar shekara inda dan kwallon Aston Billa ya zura kwallo a raga amma alkalin wasa ya ce ya yi satar fage duk da na’urar ba ta bayyana haka ba ya sa tsohon mai sharhi a kafar watsa labaran wasanni ta Sky, Sports Richard Keys ya bayyana cewa akwai yiwuwar Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta umarci Ingila ta daina amfani da na’urar ganin ba ta bin ka’idojin da suka kamata wajen amfani da ita.

Richard Keys wanda ya wallafa haka a shafin sadarwarsa na Twitter a ranar Litinin da ta wuce ya ce tuni Hukumar FIFA ya yanke shawarar tuntubar Ingila game da yiwuwar daina amfani da na’urar.

Tun bayan da aka fara amfani da na’urar BAR a Ingila ake ta samu koke-koke game da yadda alkalan wasa suke zartar da hukunci da hakan ke jefa kulob da dama cikin matsala.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya