✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a gurfanar da matasan da suka yi wa ’yar shekara 14 fyade

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta ce nan ba da dadewa ba za ta gurfanar da matasan nan hudu a gaban kotu kan zargin yi…

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta ce nan ba da dadewa ba za ta gurfanar da matasan nan hudu a gaban kotu kan zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 14 fyade a unguwar Mil 12.
’Yan sandan sun kama Wale Badejo da Jubril Yusuf da Olusanya Remi da kuma Wale Oluwafemi, wadanda shekarunsu suka kama daga 18 zuwa 19, kan zargin daukar yarinyar, wacce aka sakaya sunanta, lokacin da take kan hanyar zuwa makaranta suka yi mata fyade a ranar 30 ga watan Mayu da ya shige.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Madam Ngozi Braide ta bayyana cewa da zarar sun kammala bincike za su gurfara da su a gaban kuliya.
Ta ce, “Mun kama su kuma muna ci gaba da bincike. Duk lokacin da muka kammala bincike za mu gurfanar da su a gaban kotu, ba tare da bata lokaci ba. Ka san lamarin bincike, ba ka cewa ga lokacin da za ka kammala shi, abu ne da za a yi ta yi har sai lokacin da aka kai karshensa. Saboda haka za mu kai su kotu idan muka gama”.
Bincike ya nuna asirinsu ya tonu lokacin da suka nadi hoton bidiyon lalatar da suka yi da yarinyar a wayar salula inda daga bisani wani da ya ga abin a wayar daya daga cikin yaran da suka yi fyaden, sai ya sanar da mahaifan yarinyar.
Ita kuma ba ta yi kasa a gwiwa ba, sai ta sanar da ofishin ’yan sanda da ke unguwar Ketu inda daga bisani aka kama su.
Sai dai wata majiya ta bayyana cewa iyayen yaran suna ta lallashin mahaifiyar yarinyar mai suna Iyabo ta hakura ta janye karar ta yafe musu, amma ta dage kan ba za ta janye ba, har sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi kan cin zarafin da aka yi wa ’yarta.
Wata majiya ta bayyana cewa lamarin ba shi ne karo na farko da matasan ke yi wa ’yan mata fyade ba a yankin.