✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a haramta Babura a babban birnin Habasha

Mahukuntan  Babban Birnin kasar Habasha, wato Addis Ababa, za su haramta hawa Babura a wani yunkuri da suke na rage yawaitar aikata miyagun laifuka a…

Mahukuntan  Babban Birnin kasar Habasha, wato Addis Ababa, za su haramta hawa Babura a wani yunkuri da suke na rage yawaitar aikata miyagun laifuka a kasar.

Mahukuntan sun ce suna da yakinin cewa galibin muggan laifukan da ake aikatawa a birnin mahaya babur ne suke aikata su. Mataimakin magajin garin birnin Addis Ababa Takele Uma ya shawarci masu hawa baburan da su fara tunanin wata hanya da za su maye gurbin hawa baburan  wajen zirga-zirgarsu, kafin wa’adin haramcin ya kare a ranar 7 ga watan Yuli mai zuwa.

A cikin ’yan shekarun nan Babur ya kasance mafi saukin hanya ta sufuri a birnin, saboda kokarin kauce ma shiga cikin cinkoson ababan hawa da jama’a ke yi. Duk da yake dai ba su kai yawan wadanda ake gani a wasu manyan biranen na Afirika ba kamar birnin Nairobin kasar Kenya.

Sai wannan haramcin ba zai shafi ofisoshin jakadanci ba da kuma ma’aikatan gidajen wayan kasar.