Daily Trust Aminiya - Za a haramtawa likitocin gwamnati aiki a asibiticoci masu za
Subscribe

Gwamna Nasiru El-Rufa’i na Jihar Kaduna

Za a haramtawa likitocin gwamnati aiki a asibiticoci masu zaman kansu

Gwamnar jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce, nan bada dadewa ba gwamnatinsa zata samar da wata doka da zata haramtawa likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnatin jihar budewa ko yin aiki a asibitoci masu zaman kansu a jihar.

Ya ce, duk wanda yaga ba zai bi wannan doka ba toh yana iya ajiye aikinsa ya je ya bude asibitin nasa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani tattaunawa da ya yi da manema labarai wanda aka saka a gidajen radiyoyin jihar kai tsaye a karshen makon nan.

A cewar Gwamnan ya ce, dole ne likitocin da ke aiki asibitin gwamnati su zabi daya in ma dai ci gaba da aiki a asibitin gwamnati ko kuma a asibiti mai zaman kansa.

“Mun sani cewa aiki a asibitin gwamnati babu albashi mai kyau amma kuma akwai albarkar aiki domin akwai lada da Allah zai baka muddin kayi adalci a cikinsa. Idan kana san zama Dangote ne toh sai ka tafi amma idan kana san albarka da lada sai ka tsaya a gwamnati.” In ji shi.

Ya kara jaddada cewa, za su kira likitocin a sanar da su cewa duk wanda ya bude asibiti mai zaman kansa dole ya rufe in kuma ya zaba yin aiki asibitinsa ne toh sai ya bar aiki.

“Muna da labarin yadda mutane marasa lafiya ke zuwa asibitin gwamnati domin neman magani amma sai irin wadannan likitoci su fada masu cewa cutarsu ba tanan bane dan haka sai su turasu nasu asibitin wanda yin hakan ba daidai bane cin amana ne”. In ji shi.

texem
More Stories