Search
Subscribe
Za a horar da matasa 500 dabarun noma

Za a horar da matasa 500 dabarun noma

Akalla matasa 500 daga sassan kasar nan ne ake sa ran za a horar da su dabarun noma a Shirin Koyar da Dabarun Noma na Kasa (ASAP) a karkashin Shirin Samar wa Matasa Aikin Yi (SKYE) a zango na biyu da za a gudanar  a bana.

Babbar Daraktar Gidauniyar FarmAgric, Misis Beronica Balentine ta fadi a wurin gabatar da tsarin manhajar ta farko cewa  sun samu nasarar aiwatar da manhajar farko inda aka horar da matasa kusan 300, bayan nan shirin zai kara yawan matasn zuwa 500 da za su halarci horarwar kamar yadda aka yi a tsarin horarwa ta farko ta harkar  noman.

“Manufar da muke son cimmawa ita ce mu horar da matasa da samar musu kayan aiki domin shigo da su harkar noma da kafar dama. A halin yanzu mun horar da matasa 300 muna duba yiwuwar kara yawansu zuwa 500 a zangonmu na biyu da muka tsara da aka fara a karshen watan jiya,” inji ta.

Kan yadda za a yi rajista don shiga tsarin nasu na biyu, sai ta ce rajista da su a tsarin na biyu da aka fara za a fara karatu duk mai sha’awa yana iya kawo kansa ta hanyar adireshin gidauniyarsu na Intanet.

Daraktar ta ce akwai sha’awa daga matasa musamman mata a wurin horarwa, kashi 78 cikin 100 daga cikin matasa 300 da suka halarci horarwar  farko mata ne kuma an fahimci suna da kalubale wajen samun tallafin noma da kuma danne su da aka yi.

Ta ce gidauniyar ta himmatu wajen tabbatar da akalla kashi 30 na duk wani tallafi da za su bayar mata ne za su amfana.

Ko-odineta kan dorewar ci gaban tattalin arziki, Hans-Ludwig Bruns, ya yi magana kan shirin da Ma’aikatar Tattalin Arziki da Hadin Kai da Ci gaba ta kasar Jamus (GIZ) ta samar, wacce ake aiwatarwa da hadin gwiwar Gidauniyar FarmAgric da ke harkokin noma, ya ce ana kawo shirin ne domin tallafa wa harkar noma a tsakanin matasa.

Daya daga cikin mahalarta horarwar, Nonye Ezenwa, ya ce, “Ban taba sanin harkar noma tana da sauki ba sai a yau da wannan horarwa da na samu. Ji nake kamar in tafi gona a yanzu in yi shuka don girbe amfanin gona mai kyau. An koyar da mu ne a aikace ba a karance ne ba,  ba kawai ilimi ne aka dura mana a kwakwalenmu ba, don haka za mu iya bunkasa bangaren noma da ilimin da muka samu,” inji shi.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin