✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a iya kada kuri’a da kowace yatsa – INEC

Batun yatsar da mutane ya kamata su yi amfani da ita domin dangwala kuri’arsu a lokacin zabe na neman kawo rudani a kasar nan. Wani…

Batun yatsar da mutane ya kamata su yi amfani da ita domin dangwala kuri’arsu a lokacin zabe na neman kawo rudani a kasar nan.

Wani sako da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta musamman WhatsApp ya bayyana cewa hukumar zabe ta canja tsarin yadda mutane za su jefa kuri’a.

Cikin bayanin da ake yadawar har da yatsar da hukumar ta ce za a yi amfani da shi.

Amma Hukumar INEC ta karyata labarin inda ta ce masu zabe za su iya amfani da kowace yatsa yayin dangwala kuri’arsu.

A wani bayani da ta wallafa a shafinta na Tiwita, hukumar ta bayyana cewa masu zabe za su iya amfani da kowace yatsa su dangwala kuri’arsu kamar yadda BBC ya rawaito daga shafin.

“Mai kada kuri’a zai iya amfani da kowace yatsa domin kada kuri’arsa. Amma ya tabbatar da cewa tawadarsa tana cikin zagayen akwatin jam’iyyar da ya dangwala wa, kada ta shiga cikin akwatin wata jam’iyya daban,” inji INEC.

A wani sako da aka rika yadawa, an ce “A yanzu ba za ka dangwala kuri’a da babbar yatsa ba sai dai da dan ali wato manuniya Duk kuri’ar da aka kada da babbar yatsa za a soke ta. Tambayar a nan ita ce, me ya sa ba a wayar da kan ’yan kasa ba har yanzu? Me ya sa INEC ta boye irin wadannan bayanai masu amfani har sai kwana kadan kafin zabe?

Don Allah ba wai karantawa kawai za ku yi ba ku tura wa sababbin masu kada kuri’a don su fadaka.

Makomar kasarmu ta dogara ne a kan yatsar dan ali wato (‘’yar manuniya),” kamar yadda BBC ta rawaito yadda ake rubuta sakon na karya.