✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za a iya magance ta’addancin da ke gudana a Zamfara idan…’

Sarkin Yamman Hakimin Akuzo da ke Masarautar Wonaka ta Gabas a Karamar Hukumar Gusau da ke Jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Adam Maiyadi Jos, ya ce…

Sarkin Yamman Hakimin Akuzo da ke Masarautar Wonaka ta Gabas a Karamar Hukumar Gusau da ke Jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Adam Maiyadi Jos, ya ce in al’ummar Jihar Zamfara suka bai wa jami’an tsaro goyon baya da hadin kai za a iya magance kashe-kashen da ’yan ta’adda suke yi a jihar.

Sarkin Yamman ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos, inda ya ce ya kamata masu ruwa-da-tsaki kan harkokin mulki a Zamfara da sauran al’ummar jihar su kawar da bambance-bambancen siyasa, su hada kai da jami’an tsaro kan yaki da miyagun abubuwan da ake yi a jihar, don a samu nasarar kawo karshen kashe-kashen bayin Allah da ake yi a jihar.

Sarkin Yamman ya yaba wa jami’an tsaro kan nasarar da suka samu a kwanakin baya, inda suka kashe ’yan ta’adda sama da 50.

Ya koka kan karuwar rashin tsaro da ake fama da shi a jihar, inda ya ce yana daya daga cikin wadanda wannan matsala ta rutsa da su, domin kwanakin baya ’yan ta’addan sun kashe kanensa mai suna Alhaji Abdullahi wanda ya ya bar ’ya’ya 19.

Kuma ya ce a kwanakin baya ’yan ta’addan sun auka wa kauyensu, suka kashe mutum18. Ya ce wannan babbar barazana ce ga rayuwarsu. Don haka ya bukaci gwamnati ta taimaka musu da jami’an tsaro.