✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a mayar da Asibitin Shekoni Asibitin Koyarwa na Jami’ar Dutse

Shirye-shirye sun yi nisa wajen mika Asibitin Kwararru na Rasheed Shekoni mallakar Gwamnatin Jihar Jigawa ga Jami’ar Gwamnatin Tarayya don mayar da shi Asibitin Koyarwa…

Shirye-shirye sun yi nisa wajen mika Asibitin Kwararru na Rasheed Shekoni mallakar Gwamnatin Jihar Jigawa ga Jami’ar Gwamnatin Tarayya don mayar da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Dutse.

Ministan Lafiya, Dokta Osagie Emmanuel Ehanire ne ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci jihar, inda ya nuna gamsuwa da yadda gwamnatin jihar ta mika wa Gwamnatin Tarayya asibitin a matsayin Asibitin Koyarwa na Jami’ar.

Dokta Osagie ya ce sun zo jihar ce domin su gane wa idonsu asibitoci biyu da jihar ta ware don amfani da su, inda ya ce da zarar asibitin koyarwar ya fara aiki, za a samu kwararrun likitoci da sauran ma’aikatan lafiya wadanda za a yi alfahari da su a nan gaba a Najeriya.

A jawabin Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namaddi wanda ya karbi bakuncin Ministan da ayarinsa, ya ce sun jima suna jiran wannan lokaci da za su mika asibitin ga Hukumar Gudanarwar Jami’ar domin harkokin kiwon lafiya su bunkasa a jihar.

Ya kara da cewa an amince za a bai wa jami’ar Asibitin Shekoni tun a shekarar 2017, abin da ya rage shi ne ita hukumar jami’ar ta kammala kididdigarta a kan asibitin don fara amfani da shi.

A jawabin Mai martaba Sarkin Dutse lokacin da Ministan ya ziyarci fadarsa Alhaji Nuhu Muhammed Sunusi ya ce Jihar Jigawa tana kan gaba a fagen kiwon lafiya, kuma hakan ya samu ne da kokarin gwamnatin jihar na bunkasa harkokin kiwon lafiya.

Sarkin ya ce ilimi da kiwon lafiya su ne kashin bayan duk wata rayuwa, sannan ya ce Jihar Jigawa ce jihar da ta fi kowace jiha a Najeriya zaman lafiya duk da cewa tana kusa da jihohin da rikicin Boko Haram ya addaba a shekarun baya.

Ya kara da cewa da a ce an fara amfani da Asibitin Shekoni daga lokacin da Gwamnatin Jihar ta sha alawashin bai wa jami’ar a shekarar 2017, da tuni an fara yaye dalibai masu karatun fannin likitanci da za su rike manyan asibitoci a jihar da sauran jihohi da za a yi alfahari da su a Najeriya.