✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a rataye mai yaudarar mata yana kashe su

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga matashin nan da ya yi kaurin suna wajen kashe mata a otal a Ribas. Mai Shari’a…

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga matashin nan da ya yi kaurin suna wajen kashe mata a otal a Ribas.

Mai Shari’a Adolphus Enenebi na Babbar Kotun da ke zamanta a garin Fatakwal ya yanke hukuncin ne bayan samun Gracious David West da laifuka shidan da ake tuhumar sa.

Da yake yanke hukuncin a ranar Jama’a, alkalin ya ce hujjojin da aka gabatar sun gamsar da kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifukan.

Sai dai ya sallami mutum na biyu da ake zargi a shari’ar, Nimi ThankGod ya kuma wanke shi daga laifi, saboda rashin kwararan hujjoji.

An gurfanar da Gracious David West ne bisa zarginsa da yaudarar mata a lokuta yana kai su otel yana kashe su daban-daban a garin Fatakwal.