✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a samar da cibiyar gwajin coronavirus a Sakkwato

Kwamishinan lafiya na jihar Sakkwato kuma shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a Sakkwato, Dakta Muhammad Ali Inname, ya ce nan da kwana biyu za…

Kwamishinan lafiya na jihar Sakkwato kuma shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a Sakkwato, Dakta Muhammad Ali Inname, ya ce nan da kwana biyu za a samar da cibiya don fara gwajin cutar a Sakkwato domin bukatar yanda za a shawo hana bazuwar cutar.

Kwamishinan, ya bayyana hakan ne a taron manema labarai ranar Talata da ta gabata ya fadawa al’umma su kwantar da hankalinsu majiyancin da aka samu da cutar coronavirus yana murmurewa, kuma suna kan aikin tattara duk wanda mai cutar ya yi mu’amala da su domin yi wa tufkar hanci.

Inname, ya nuna sun tsundumma sosai wajen gano inda cutar ta samu wannan mutumin ganin ba inda ya fita, nan da kwana biyu za a samar da cibiya don fara gwajin cutar a Sakkwato.

“Kan wannan aikin jami’an Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun zo Sakkwato yanzu haka.” in ji Kwamishinan.

Kwamishina ya bayyanawa al’ummar Sakkwato, Alhaji Musa Bashar wanda aka fi sani da Rahamaniya a labarin da suka samu ya koma Abuja kamar yadda gwamna ya bukata bai shigo ba.

Kwamishina, ya ce a zuwa yanzu ba su gama haɗa yawan mutanen da suka yi hulda da shi ba amma da zaran sun gama za su yi wa al’umma bayanin yawan da halin da ake ciki.

Ya ce, sun fara yiwa asibitocin gwamnati feshin kashe kwayoyin cutar, sun soma magana da asibitoci masu zaman kansu kan yin feshin.

“Cibiyar horas da masu yiwa kasa hidima NYSC da ke Wamakko mun mayar da ita wurin killace wadanda suka shigo jihar nan ta barauniyar hanya za a ajiye su a duba yanayin lafiyarsu kafin a bari su tafi, mun karbi kira yafi 100 kan cutar coronavirus  abin da ke nuna mutane sun fadaka da yarda da ciwon nan gaskiya ne a hada kai domin yakarsa.” a cewarsa.

Kan shigowa cikin garin Sakkwato da ake yi ya ce za su hada kai da sarakunan gargajiya domin shawo kan lamarin.