Search
Subscribe
Za a yi wa jaririyar da aka yi wa fyade tiyata

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu

Za a yi wa jaririyar da aka yi wa fyade tiyata

Jaririya ‘yar wata uku da aka yi wa fyade a Jihar Nasarawa na hanyarta ta zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos inda za a yi mata tiyata a al’aurarta da duburarta da mai fyaden ya lalata.

Mahaifiyar jaririyar ce ta shaida wa wakilinmu haka, tana mai rokon jama’a da su taimaka da abin da za a yi wa diyar tata aikin domin ceton rayuwarta.

“Muna hanyar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) inda za a yi mata tiyata”, inji ta, tana mai yaba gudunmuwar  da jama’a suka yi domin a fara aikin.

Aminiya ta kawo muku labarin yadda aka sace jaririyar da tsakar dare aka yi mata fyade aka kuma jefar da ita a wani kango, a kauyen Adogi na jihar Nasarawa.

Daga bisani rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta kama wani matashi da take zargi shi ne ya lalata jaririyar.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin