✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za ku iya komawa fadar Olubadan ne idan kun tube rawanin sarautar bogi – Olubadan

Mai martaba Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji ya shaida wa manyan ’yan Majalisar Sarki 8 da hakimai 13 da Gwamnatin Jihar Oyo ta daukaka…

Mai martaba Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji ya shaida wa manyan ’yan Majalisar Sarki 8 da hakimai 13 da Gwamnatin Jihar Oyo ta daukaka darajarsu zuwa sarakuna a bara cewa, idan suna son dawowa Fadar Sarkin a matsayin halattattun ’yan majalisar masarautar Ibadan, wajibi ne su tube haramtattun rawunan sarautar tare da neman gafarar al’ummar Ibadan da Yarbawan gaba daya kafin a karbe su.

Bayanin haka yana kunshe ne cikin wata takardar sanarwa da ta fito daga Fadar Olubadan a ranar Talata inda fadar ta mayar da martani a kan zargin da sarakunan suka yi wa Olubadan  na Ibadan  cewa, shi ne ya hargitsa majalisar saboda son ransa. Ya tsame hannunsa daga batun kaurace wa fadarsa da sababbin sarakuna suka yi.

Ya ce, daukar matakin kaurace wa fadar da suka yi alama ce ta wulakanta Masarautar Ibadan.  Sanarwar dauke da sanya hannun Daraktan Hulda da Jama’a na fadar Mista Adeola Oloko ta ruwaito Olubadan yana cewa: “Na yi tsammanin  manyan ’yan Majalisar Sarki za su girmama hukuncin da Babbar Kotun Jihar Oyo ta zartar cewa daukaka darajarsu zuwa sarakuna da gwamnatin jihar ta yi haramtacce ne domin a kasar Yarbawa babu garin da sarakuna biyu suke mulki.”