Da Dumi Dumi

Za mu bude rugage a kowane bangare na Najeriya –  Danladi Pasali

Ganin cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa Ma’aikatar Gona ta Tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) umarnin su shigar da kwararru masu zaman kansu, kan  shirin samar da wuraren kiwo, na Ruga, ’ya’yan Kungiyar Yakin Zaben Shugaban Muhammadu Buhari, ta Buhari Campaign Organization (BCO), sun yunkuro don samar da gonakin Ruga, a kowanne bangare na kasar nan.                                                                                                                                                          Shugaban Kungiyar BCO ta Kasa Alhaji Danladi Garba Pasali ne ya bayyana haka, lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos, fadar Jihar Filato.

Alhaji Danladi Pasali ya ce “Dama muna da bangaren tallafa wa ’ya’yan  wannan kungiya, kan aikin noma. Kuma a wannan bangare muna da shirin harkokin  kiwon shanu da kiwon kifi da sauran harkokin noma.”

Ya ce yanzu gwamnati ta ce wannan shiri na Ruga ba sai gwamnatocin jihohi kadai ba. ’Yan kasuwa ko kwararru kan harkokin noma za su iya shiga wannan shiri. Kuma gwamnati za ta ba su lasisi su je su yi wannan shiri  nasu na kansu.

“Don haka wannan kungiya ta samu wadansu ’ya’yanta masu  yawa  daga sassan Yarbawa da Ibo da Arewacin Najeriya da suka nuna bukatarsu na shiga wannan shiri. Tuni wadannan ’ya’yan kungiya sun bayyana niyyarsu ta samar da shanu da filayen da za su yi harkokin kiwo a karkashin wannan shiri na Ruga,” inji shi.

Alhaji Pasali, ya ce babu idan ’yan Najeriya suka rungumi shirin, Najeriya za ta rika fitar da madara da nama zuwa kasashen waje.

ADVERTISEMENT

Ya yi kira ga al’ummar Najeriya kan kowa ya koma kan harkar noma, domin taimaka wa kasa da al’umma ga baki daya.

Share