Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Za mu bude wuraren koya wa matasa sana’a a Katsina – Kungiyar Masu Walda

Kungiyar Masu Walda

Za mu bude wuraren koya wa matasa sana’a a Katsina – Kungiyar Masu Walda

Kungiyar Masu Sana’ar Walda da Kere-Kere ta Jihar Katsina, tana yunkurin bude wuraren da za ta koya wa matasa sana’ar walda a tsofaffin kananan hukumomin jihar domin ta rage wa matasa zaman kashe wando.

Shugaban Kungiyar Alhaji Sani Ado Kwa, wanda aka fi sani da Sanado ya shaida wa Aminiya haka a ofishinsa a Katsina.

Ya ce: “Muna nan muna shirin bude wuraren koyar da sana’ar walda a kananan hukumomin Katsina da Daura da Mani da Kankiya da Dutsinma da Malumfashi da kuma Funtuwa, inda muke sa ran sauran kananan hukumomin da ke zagaye da su za su kawo matasansu babbar cibiyar da ke yankinsu. Gwamnati ma na iya kawo dalibanta masu koyon sana’ar tamu domin ba su horo.”

Shugaban ya ce wannan na daga cikin irin godiya da yabon da za su yi wa gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari kan gudunmawar da yake ba kungiyar tasu.

“Tun farkon hawan wannan gwamnati, Gwamna Masari ya ba wannan kungiya aikin hada kujeru. Har ila yau, Gwamnan ya ba wa wannan kungiya taimakon injunan walda; wadanda muka rarraba su a kananan hukumomi kuma kyauta. Bayan wannan, an sake ba mu wani aikin na miliyoyin naira karo na biyu kuma mun raba su a tsakanin mambobinmu ban da wanda aka ba kamfanina wanda shi ma na raba wa ’yan kungiyar don kada a zauna haka nan. Sa’anna ga wani aikin da ake cikin shirye-shiryen ci gaba da shi. To in kuwa har ba mu fito mu ma muka nuna gwamnati jin dadi tare da taimaka mata ba, musamman ta samar da abin yi ga matasanmu, ai da ba mu kyauta ba,” inji Shugaban.

Ya ce, bisa lura da yawan ayyukan assha da matasan ke yi da suke danganta haka da rashin aikin yi ne ya sa suke kokarin bude wadannan cibiyoyi da suke ganin za su taimaka kwarai wajen magance matsalar; musamman ta hanyar dauke hankulan matasan zuwa ga aiki maimakon su rika tunanin wasu abubuwa da kan sanya su shiga ayyukan ta’addanci.

“Kungiya ta lura cewa, Gwamna Bello Masari mutum ne mai son kawo ci gaba a jihar nan ta kowace fuska; bisa wannan hange ne ya sa ya zama wajibi ga kowa a jihar nan a kungiyance ko a daidaiku mu fito da duk wani abin da Allah Ya hore mana domin ganin mun tallafa. Gaskiyar magana, abubuwa sun yi wa gwamnati yawa,” inji Shugaban. Game da korafin da wadansu ’ya’yan kungiyar ke yi; cewa, an dauke su kamar ba ’ya’yan kungiyar ba domin sai dai su ji wai, Shugaban ya ce, “Duk wadanda ke wannan koke a yanzu, irin su ne wadanda aka ba aiki a wancan lokacin wadansu ba su yi aikin ba, wadansu kuma sun yi ha’inci a kan yadda aka ce a yi, yayin da wadansu ko ganinsu a kowane irin aiki na kungiyar ko taro ba a yi, sai sun ji an ce ga wani abu. Ta yaya za a ce a ba irin wadannan aiki?”

Ya ce: “Ba zan manta ba,  lokacin da kungiyar ta yi aikin  gayya na gyaran tebura da kujeru da kyamaren wasu makarantu a jihar domin tallafa wa gwamnati, wadansu ko kallo ba mu ishe su ba. To ka ga aikin kungiya na yiwuwa a haka?”