✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ci gaba da yakar PDP daga cikinta – Gwamna Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce kaurace wa Jam’iyyar PDP da gwamnoni biyar suka yi da kuma sauran biyun da suka ki komawa…

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce kaurace wa Jam’iyyar PDP da gwamnoni biyar suka yi da kuma sauran biyun da suka ki komawa APC wata ishara ce ga Jami’yyar PDP, domin matakin da suka dauka zai zame wa jam’iyyar alakakai. Gwamna Lamido ya ce ficewar takwarorinsa wani salo ne na siyasa da zai hana PDP zaman lafiya domin su da suka fice za su je waje suna yakar jam’iyyar,  shi da dan uwansa da suka rage a cikinta kuma suna ciki suna yakarta, inda ya ce sun dauki matakin haka ne da nufin tarwatsa tsarin jam’iyyar ta PDP. Gwamna Lamido ya nuna damuwa game da fushin da gwamnoni biyar suka yi suka fice daga jam’iyyar, inda ya ce Bamanga ne matsalar PDP, “saboda haka har gobe ina nan ina yaki da su Bamanga ba zan daina ba domin sauran gwamnonin da suka fice sun yi bauta ga PDP kuma suna sonta amma matsalarsu Bamanga ne shi ya sa suka fice daga jam’iyyar,” inji shi. Ya ce Bamanga ya dauko tsarin cin mutunci a cikin Jam’iyyar PDP, kuma haka ne ya sa suka fice daga jam’iyyar ba domin ba sa son ba, sai saboda halayyar Bamanga, “yanzu fitarsu za ta zame wa su Bamanga wata ishara da za ta iya zama darasi a wajen magoya bayan jam’iyyar,” inji Lamido.